Wasu suna ganin Shugaba Tinubu ya bambanta da Buhari ta fuskar zafin nama.  Hoto: Shugaba Tinubu Facebook

'Yan Nijeriya suna ci gaba da jiran sunayen mutanen da Shugaba Bola Tinubu zai nada a matsayin sabbin ministocinsa, duk da cewa saura kasa da kwana 20 wa'adin da doka ta dibar masa don ya yi hakan ya cika.

Sai dai idan aka yi la'akari da sunan da 'yan kasar da suka sanya masa na "Baba Go Fast," wato shugaban da ke da zafin-nama wajen daukar mataki, kamar yadda ya nuna a farkon hawansa wajen daukar wasu zafafan matakai, wasu suna ganin lokaci ya yi da ya kamata shugaban ya kafa majalisar ministocinsa.

Ko da yake Shugaba Muhammadu Buhari a wa'adinsa na farko a shekarar 2015, sai da ya kwashe kusan wata shida kafin ya nada nasa ministocin.

Wasu suna ganin Shugaba Tinubu ya bambanta da Buhari ta fuskar zafin-nama, misali a ranar da aka rantsar da shi ya sanar da cire tallafin mai wanda gwamnatocin da suka gabace shi suka kasa yi.

Bayan 'yan makonni kuma ya sanar da dakatar da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele da kuma Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa da Shugaban Hukumar Kwastam Hameed Ali da kuma sauke manyan hafsoshin tsaron kasar.

'Tinubu yana da sauran lokaci'

Babban Mai Taimaka wa Shugaba Tinubu kan hulda da 'yan jarida Malam Abdulaziz Abdulaziz ya shaida wa TRT Afrika cewa babban abin da Shugaba Tinubu ya sanya a gaba tun bayan dawowarsa daga Guinea-Bissau a ranar Litinin shi ne "tattara sunayen ministocin da zai nada.

Yana kara tantance su ne kafin ya tura mataki na gaba, wato ya aika wa majalisar dattawa don neman yardarta."

Malam Abdulaziz ya ci gaba da cewa tantance sunayen ne ya jawo tsaiko "saboda Nijeriya kasa ce mai yawan jama'a sosai kuma a ciki mutum 42 kacal za a zabo.

Dole idan ba a natsu ba sai a yi kitso da kwarkwata. Akwai kuma tantancewa na abubuwa da dama — na farko dai kokarin duba wadanda suka dace da masu kwarewa da duba gudunmawar da wasu 'yan siyasa suka bayar."

"Ana kokarin a samu daidaito tsakanin kwarewar mutum da kuma sakayya ga 'yan siyasa wadanda suka taka rawa wajen kawo wannan gwamnati kan katagar mulki. Duk wadannan abubuwa ne da sai an duba su a tsanake.

Haka nan kuma akwai bincike na tsaro domin tabbatar da kyan hali da kuma tabbatar da cewa mutum ba shi da wata matsala, wanda wannan bincike jami'an tsaro ne suke gudanarwa.

To duka sai an gabatar da wannan, an tabbatar da cewa babu matsala kafin a tattara wadannan sunaye a mika wa majalisar dattawan kasar," in ji Malam Abdulaziz Abdulaziz.

'Zabar ministoci ba abu ne mai sauki ba'

Masani kan harkokin siyasa wanda yake Jami'ar Abuja Dokta Abubakar Kari ya ce "abin da wannan yake nufi shi ne ba abu ne mai sauki ba zabar ministoci.

Wato ba kamar sauke mutane a mukamai ba. Nada sabbi musamman a wurin sabuwar gwamnati abu ne wanda sai an bi a hankali."

Dokta Kari ya ce akwai abubuwa da dama da ake la'akari da su wajen zabar ministoci kamar: "jiha da bangaranci da addini da cancanta da bauta wa jam'iyya da sauransu,"in ji masanin harkokin siyasar.

"Dole ne Tinubu ya dauki lokaci. Idan ya ciza, ya wura. Sannan ya daddale ya duba dukkan wadannan lamura kafin ya mika wadannan sunaye.

"Kuma kasancewa har zuwa yanzu bai mika wadannan sunaye ba, to tabbaci ne cewa shi kansa bai samu batun da sauki ba. Abin ba mai sauki ba ne, yana da sarkakiya kwarai da gaske," in ji Dokta Kari.

A karshe masanin ya ce tsarin mulkin kasar, kamar yadda aka yi masa gyara a bara, ya bukaci kada a wuce wa'adin kwana 60 wajen nada sabbin ministoci bayan rantsar da sabuwar gwamnati.

"Zuwa yanzu an yi fiye da kwana 40, ka ga kenan Shugaba Tinubu yana da sauran kwana kasa da 20 na ya kammala wannna aiki.

"Wanda tilas ne ya kammala aikin ya kuma tura jerin sunayen wadanda yake so su zama masa ministoci zuwa majalisar dattawa wadda za ta daddale su. Kuma ina da yakinin cewa a cikin kasa da kwana 20 wannan zai yiwu," in ji Dokta Kari.

TRT Afrika