Rundunar Sojin Sudan ta ce babban kwamandanta, Janaral Abdel Fattah al-Burhan, ya tsallake rijiya da baya yayin wani hari da jirage biyu mara matuƙa suka kai a wajen taron yaye sojoji ɗalibai a gabashin ƙasar inda aka kashe mutane biyar.
Rundunar Sojin Sudan ta ce harin na jiragen yaƙi marasa matuƙa sun auku ne a Gebeit, wani gari da ke gabashin Sudan, bayan kammala bikin yaye ɗalibai sojoji.
Burhan, wanda ya halarci bikin yaye ɗaliban sojoji ya kuɓuta ba tare da samun ko ƙwarzane ba, in ji Laftanal Kanal Hassan Ibrahim, daga ofishin kakakin rundunar sojin.
Sama da shekara guda kenan aka kwashe ana gwabza yaƙi a Sudan tsakanin dakarun sojin ƙasar da mayakan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta RSF.
Babbar cibiya a gabashin ƙasar
Sakamakon arangama a babban birnin Khartoum, sojojin ƙasar da gwamnati suna gudanar da mafi yawan ayyuka a wajen gabashin Sudan kusa da Tekun Maliya.
Wannan hari na jirage mara matuƙa shi ne na baya-bayan nan a irin waɗannan hare-hare da ake kai wa cibiyar sojoji, kuma mafi kusanci da Port Sudan.
Dakrun RSF ba su ce komai game da wannan hari ba kawo yanzu.
Harin ya zo ne kwana guda bayan da ma'aikatar harkokin waje da ke ƙarƙashin rundunar sojin ta amsa gayyatar tattaunawar sulhu da Amurka ta miƙa musu wadda za a yi a Switzerland a watan Agusta.
RSF ta ce za ta yi sulhu da sojoji ne kawai, ba wai da masu kishin Musulunci da suke da adadi mai yawa a ayyukan gwamnati ba.