Abba Kabir Yusuf  ya yi kira ga hukumar Hisbah ta yi koyi da wasu hukumomin da ke wanzar da wajen gudanar da ayyukanta./Hoto: Abba Kabir Yusuf/Facebook

Gwamnan Kano da ke arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya ce hukumar Hisbah ta jihar tana aikata "kuskure babba" game da yadda take gudanar da wasu ayyukanta a yunƙurin yaƙi da masu aikata ɓarna.

Ya bayyana haka ne ranar Alhamis da maraice lokacin da yake ganawa da wasu Malaman addinin Musulunci a gidan gwamnatin jihar.

Gwamna Abba Gida-Gida, kamar yadda aka fi saninsa, ya ce akwai kura-kurai da dama a salon da Hisbah take bi wurin kama masu aikata ɓarna musamman mata da matasa.

''An je inda wasu matasa ke ɓarna - maza da mata - amma yadda aka dinga ɗebo su ana duka da gora, suna gudu ana bin su da gora ana taɗe ƙafafunsu, ana ɗebo su kamar awaki a jefa su cikin mota (Hilux), wannan muna gani kuskure ne babba,'' a cewar gwamnan na jihar Kano.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta miƙa amanar gyaran al'umma ga hukumar Hisbah don haka ya kamata ta riƙe aikinta cikin gaskiya da amana.

Gwamna Abba Kabir ya ce: "Hisbah hukuma ce wadda muka ɗauke ta da martaba, kuma muka ɗebo bayin Allah waɗanda muka san za su iya muka ce ga amanar al'ummar jihar Kano amma ma'anar yin hukuma shi ne a yi abin da yake daidai".

Ya yi kira ga hukumar ta yi koyi da wasu hukumomin da ke wanzar da wajen gudanar da ayyukanta, yana mai ƙarawa da cewa ya kamata ta riƙa haɗa gwiwa da jami'an ƴan sanda da DSS da sauransu yayin da za ta kai samame.

TRT Afrika