| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeirya sun gano albarusai masu yawa a cikin kwata a Maiduguri
Hukumomi sun ce tuni aka dauki matakin tabbatar da cewa lamarin bai jefe rayuwar jama’a cikin hadari ba, yayin da ake ci gaba da yunƙurin kwashe ruwan da ke cikin kwatar ko za a gano wasu karin makaman.
Sojojin Nijeirya sun gano albarusai masu yawa a cikin kwata a Maiduguri
An gano makaman ne a cikin wata kwata a ungwar Bulumkutu a birnin Maiduguri
3 Janairu 2026

Rundunar sojan Nijeriya ta ce ta gano tulin miyagun albarusai a cikin kwata a unguwar Bulumkutu, a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Wata sanarwa da Jami’in Watsa Labarai na Rundunar Hadin Kai da ke arewa maso gabas Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar da yammacin Asabar ta ce, an samu nasarar gano makaman ne a ranar 2 ga Janairu sakamakon bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu, kuma suka yi aiki da su.

Masu AlakaTRT Afrika - Boko Haram: Ana cin Borno da yaki, in ji Zulum

“Gano makaman ya biyo bayan ci gaba da kasancewa a yankin da dakaru suka yi, bayan killace shi da binciken ƙwaƙwaf da dakarun suka yi, sakamakon samun bayanan sirri, da nufin hana masu aikata laifuka da ‘yanta’adda sakewa su yi ɓarna, musamman ma bayan hallaka ‘yan kunar bakin wake da dama ko kama su a makon jiya,” a cewar Sani Uba.

Ya ce binciken ƙwaƙwaf a yankin ya kai ga gano albarusai 1,270 a cikin wata magudanar ruwa.

Sanarwar ta ce tuni aka ɗauki matakin tabbatar da cewa lamarin bai jefe rayuwar jama’a cikin haɗari ba, “yayin da ake ci gaba da yunƙurin kwashe ruwan da ke cikin kwatar ko za a gano wasu ƙarin makaman.”

Jami’in na soja ya ce an tura dakaru da ƙwararru kan abubuwa masu fashewa daga rundunar ‘yansandan Nijeriya don tabbatar da cewa lamarin bai haifar da wata illa ga jama’a ba.