An kammala jefa kuri’a a akasarin kasashen Turai da Amurka da kuma Canada a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Turkiyya da ke tafe.
An rufe rumfunan zabe a ofisoshin diflomasiyya a kasashen Turai da dama da ke Amurka da Canada da misalin karfe 9:00 na dare agogon kasashen, wato karfe 7:00 na dare agogon GMT a ranar Lahadi.
An ci gaba da jefa kuri’a a kasashen Austriya da Denmark da Faransa da Jamus da Luxembourg a ranar Lahadi da misalin 9:00 na safe zuwa 9:00 na dare.
An rufe zabe a kasashen Albania da Belarus da Belgium da Herzegovina da Bulgaria da Czech Republic da Estonia da Finland da Girka da Hungary da Ireland da Italiya da Kosovo da Lithuania da Malta da Moldova.
Sauran sun hada da Montenegro da North Macedonia da Netherlands da Norway da Poland da Portugal da Romania da Serbia da Slovakia da Spain da Sweden da Switzerland da kuma Birtaniya.
Kusan mutum 127,000 ne suka kada kuri’a a Birtaniya a akwatunan zabe da aka samar a biranen Landan da Manchester da Edinburgh da Leicester tun daga 29 ga watan Afrilu zuwa 7 ga watan Mayu.
A Amurka kuwa, an samar da wuraren zabe bakwai tun daga 29 ga watan Mayu zuwa bakwai ga watan Afrilu a ofisoshin jakadanci da suka hada da ofishin jakadancin Turkiyya da ke Washington, da kuma kananan ofisoshin jakadancin kasar da ke New York da Boston da Chicago da Houston da Miami da kuma Los Angeles.
Haka kuma akwai masu zabe 1,392 wadanda suke da rajista a Afirka ta Kudu da suka jefa kuri’arsu a Pretoria da Cape Town daga 6 zuwa 7 ga watan Mayu.
Zuwa ranar Lahadi, sama da Turkawa miliyan 1.6 da suke zama a kasashen waje ne suka kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar wakilan kasar, kamar yadda hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta tabbatar.
A cikin Turkiyya kuwa, za a gudanar da babban zaben a ranar 14 ga watan Mayu.
Masu zaben za su zabi tsakanin ‘yan takara hudu: Shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan wanda ke neman wani wa’adin, sai shugaban ‘yan adawa Kemal Kilicdaroglu sai Muharrem Ince da kuma Sinan Ogan.
Haka kuma akwai jam’iyyu 24 da kuma ‘yan takara masu zaman kansu 151 da ke neman kujeru 600 na majalisar kasar.
Sai dai za a ci gaba da gudanar da zabe a Austriya da Denmark da Faransa da Jamus da Luxembourg har zuwa ranar Talata, daga 9:00 na safe zuwa 9:00 na dare agogon kasar.