Kakakin jam'iyyar AK Party ta kasar Turkiyya Omer Celik ya soki kasashen da ke cewa "Israila tana da 'yancin kare kanta" amma suka yi shiru kan "damar da" mata da kananan yara a Gaza suke da ita ta ci gaba da rayuwa.
A sanarwar da ya wallafa a shafin X ranar Talata, Celik, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jam'iyyar AK Party, ya yi mummunar suka game da hare-haren da ake kai wa kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba sannan ya bayyana shirun da wasu kasashen duniya suka yi kan gallazawar da ake yi wa Falasdinawa a Gaza a matsayin "laifi a kan bil'adama."
"Damar kare kai ba daidai ba ce da kai hari kan daukacin al'umma da fararen-hula da ba su ji ba ba su gani ba," in ji Celik, yana mai bayyana cin zarafin da ake yi wa daukacin al'ummar Gaza a matsayin "laifi."
'Kawo karshen harin bama-bamai na rashin kan gado a Gaza'
Kakakin jam'iyyar AK ya bayyana tasirin hare-hare ta kasa da ake kai wa a Gaza, yana mai gargadi cewa za su iya haifar da gagarumin bala'i ga dan'adam da kuma rasa dimbin rayuka, musamman na kananan yara da mata da ba su da laifi sannan ya yi kira a gaggauta kawo karshen hare-haren rashin kan gado da ake kai wa a Gaza.
Kazalika ya soki wadanda ke mayar da hankali kan siyasar yankin fiye da neman a samar da zaman lafiya da daidaito, yana mai zargin cewa "mata da kananan yara ne suke dandana kudarsu kan siyasar da ake yi game da batun."
Ya bayyana cewa amfani da karfin soji da kuma kalaman tunzurawa za su ta'azzara halin da ake ciki maimaikon shawo kan rikicin. "Wadanda ba su da hannu a yakin sun fi shan wahalarsa.
"A yau, mun tsaya a nan ne domin kira a samu zaman lafiya da adalci," in ji kakakin jam'iyyar AK. Ya yi kira a daina kai hare-hare kan al'ummar Gaza, yana mai jaddada neman kowa ya sa baki don kawo karshen rikicin.
"Tura jiragen yaki na sama da na ruwa yankin da kuma yin barazana a kullum ba za su samar da zaman lafiya ba; za su haddasa sabon rikici ne," a cewarsa, yana mai sukar Amurka da Birtaniya da yin hakan.
Celik ya yi kalaman ne a yayin da ake ci gaba nuna fargaba game da halin rashin jnkai da ake ciki a Gaza da kuma yin kira ga kasashen duniya domin daukar mataki a kan wannan mummunan hali.
Turkiyya tana kokari sosai wajen ganin an yi tattaunawar kawo karshen rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinawa kuma tana ci gaba da fafatukar neman ganin an samu zaman lafiya a yankin.