Jam'iyyun siyasa za su aike da gwamman dubunnan masu sanya idanu a cibiyoyin jefa kuri'a. /Hoto: AA Archive

Masu jefa kuri'a a Turkiyya za su zabi magadan gari da magadan garin gundumomi da masu unguwanni a zabukan.

Tare da jam'yyu 35 da suke takara a zabukan, Hukumar Zabe ta Koli ta bayyana cewa kuri'u 350 ne kadai za a jefa a kowanne akwatin zabe a yayin zabukan gama-gari da kanana.

Wannan mataki ya dogara ne kan fahimtar cewa masu jefa kuri'a a akwatin zabe za su iya jefa kuri'a a lokacin nau'in zabuka biyu.

Muna kokarin ganin an gudanar da sahihin zabe na gaskiya a Turkiyya.

Gudanar da zabuka

Hukumar zabe ta YSK ta samar da wani tsari na tabbatar da ingancin kuri'u, farawa daga akwatunan zabe.

A kowanne bakin akwati, akwai mutane biyar da suka hada da wakilan YSK da na manyan jam'yyun siyasa na zaune don sanya idanu. Mutanen na duba katin dan aksa na mutum da tabbatar da akwai sunansa a rejistar zabe.

Wannan na hana mutum ya jefa kuri'a sau biyu. Yana kuma taimaka wa wajen amincewa da sakamako tsakanin wakilan jam'yyu da ke wajen.

Jam'yyun siyasa, ciki har da jam'iyya mai mulki ta AKP da babbar jam'yyar adawa ta CHP, suna tura gwamman dubunnan masu sanya idanu zuwa cibiyoyin jefa kuri'a.

Dubban masu sanya idanu za su bibiyi zabukan

A yayin da zabukan ke ƙaratowa, jam'iyyun sun dauki 'yan sa-kai, musamman don wannan manufa. Wadannan wakilai na da izinin su raka kuri'u zuwa wajen sanar da sakamako.

Baya ga wakilan jam'iyya da na Hukumar Zabe, kungiyoyi masu zaman kansu ma na da nasu 'yan sa-kai da suke sanya idanu kan zaben.

A lokacin da aka fara kirga kuri'u, wakilai 'yan sa-kai na jam'iyyu na zaune a wajen. Za su iya tabbatar da ko kuri'un da aka kirga sun yi daidai da sakamakon da ke hannun su ko akasin haka, za su iya daukar hotuna tare da mika bayanai ga jagororin jam'iyya na sama.

Abin da ya sanya gudanar da zaben zama mara rikici shi ne wanzuwa masu sanya idanu masu cin gashin kansu, ciki har da mutane 40 daga Majalisar Tarayyar Turai, da kuma Kungiyar Hadin Kan Tsaro ta Turai, wadanda suke zuwa bisa gayyatar da gwamnati ta yi musu.

A farkon wannan watan aka sake tabbatar da 'yancin YSK, a lokacin da ta ki amincewa da bukatar gwamnati na sanin wajen da aka ajje kuri'u, a yayin da ake sauraren gudanar da zaben.

'Yan adawa sun nuna rashin amincewa kan lallai kar a sanar da Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida a ina kuri'un suke.

Wannan na nuni da cewa ma'aikatar hukumar zabe na gudanar da ayyukansu busa 'yanci ba tare da katsalandan din gwamnati ko jami'anta ba.

Domin kauce wa duk wani nau'i na rikici, kamfanin dillancin labarai na Anadolu mallakin gwamnati ne kadai aka yarda ya saki sakamakon zabe.

TRT Afrika