An yi ƙiyasin cewa lita ɗaya ta magani wadda aka samu daga gubar kunama za a iya sayar da ita kusan dala miliyan goma. / Hoto:AA

Hukumomin Turkiyya sun kama Lorenzo Prendini, wani mai kula da wani gidan tarihi na Amurka a birnin Santambul, kan zargin yunƙurin fasa-ƙwarin wasu ƙwari masu dafi na Turkiyya zuwa ƙasar waje.

‘Yan sandan Santambul a ranar Litinin sun shirya wani samame a ranar Litinin a filin jirgin Santambul bayan gano yunƙurin fasa-ƙwaurin ƙwarin zuwa ƙasar waje.

An tsare Prendini a lokacin samamen inda aka gano kwalaben roba 88 ɗauke da ruwa inda a ciki akwai wasu ledoji 58 ɗauke da kunama 1,500 da gizo-gizo duk na Turkiyya waɗanda aka kama a cikin kayansa.

Wanda ake zargin wanda shi ne mai kula da gidan tarihin na Amurka, akwai yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu domin tuhumarsa kan saɓa dokokin fasa-ƙwarin Turkiyya.

Ana iya amfani da bayanan ƙwayoyin halitta na dabbobi masu guba na Turkiyya domin samar da magunguna.

An yi ƙiyasin cewa lita ɗaya ta magani wadda aka samu daga gubar kunama za a iya sayar da ita kusan dala miliyan goma.

TRT World