Wasu wasu mutum 42 ƴan ƙasar Turkiyya da aka kwashe daga Gaza sun isa birnin Istanbul daga ƙasar Masar.
An yi wa Turkawan maraba ta hanyar miƙa musu furanni a filin jirgin samam inda jakadiyar kasar Ayse Sozen Usluer ta tare su a ranar Lahadi.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ce ta yi kokarin fitarsu daga Gaza aka kuma kwashe su a jirgin saman Turkiyya daga filin jirgin saman Alkahira a Masar.
"Muna miƙa saƙon ta'azziyyarmu ga shaihdan da aka kashe a Gaza, da yi wa danginsu jaje da kuma fatan waɗanda suka jikkata su samu lafiya," kamar yadda Ambasada Usluer ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Ta ƙara da cewa "Ma'aikatar Harkokin Waje da gwamnatin Turkiyya za su ci gaba da ƙoƙrinsu don ganin an kawo ƙarshen wannan cin zali da ake yi a Gaza."
Kamar yadda kuka sani, nan da nan bayan rikicin ya ɓarke, mun samu nasarar kwashe ‘yan kasarmu 30, amma saboda rufe Mashigar Kan iyakar Rafah, sai aka katse. Duk da haka, kokarinmu na diflomasiyya a bayan fage ya ci gaba ba tare da tsaiko ba.
A halin yanzu, muna ba da damar sake dawo da wasu mutum 42 zuwa kasarmu. Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya na ci gaba da bayar da gudunmawar gudun hijira daga yankunan da ake fama da rikici, ciki har da 'yan kasar Turkiyya da 'yan kasashe ƙawayenmu," in ji ta.
Wadanda aka kwashe sun gode wa Turkiyya
Usame Darabeh wanda ke cikin wadanda aka kwaso ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa ya je Gaza ne domin jana'izar mahaifinsa kuma ya makale a can lokacin da aka fara kai hare-haren.
"Mahaifina ya rasu kafin a fara yakin. Na je Gaza ne don halartar jana’izarsa, kuma a lokacin ne aka fara yakin,” in ji Darabeh, wanda ya fara zuwa Turkiyya a matsayin dalibin Falasdinu mai karatun injiniyan kwamfuta, sannan kuma ya auri abokiyar karatunsa.
"An shirya kwashe mu, amma sojojin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a kan iyakar Masar," ya kara da cewa "Saboda hadarin haka ya sa duk muka dawo."
“Saboda harin bama-bamai da Isra’ila ke yi, mun koma kudancin Gaza. A wannan lokacin, nakan yi magana ta waya da matata a Samsun. Ta kasance tana tuntubar hukumomi a kasarmu a ko yaushe,” in ji shi, yana bayyana yadda daga baya ya koma Turkiyya ta hanyar tsallaka kan iyakar Masar.
Ya kuma nuna jin dadinsa ga hukumar bayar da agajin gaggawa ta Turkiyya (AFAD) da ta yi wa kungiyar maraba a bangaren Masar, inda ya ce jami’an AFAD sun ba su kulawa sosai, sannan suka yi shirin komawa Turkiyya.
"Matata za ta haihu nan da sati biyu. Za ta haifi 'ya mace. Zan kasance a wurin lokacin da aka haife ta. Na gode wa duk wanda ya yi silar da zan ji dadin kasancewar hakan. Ga mahaifiyata da ’yan uwana da suka rage, ina kuma neman taimako daga gwamnatinmu,” in ji shi, yana mai nuna farin cikinsa da komawa gida.
Bayan sun wuce sashen kula da fasfo a dilin jirgin sama, sai aka kai mazauna Istanbul gidajensu, su kuma sauran sai jami’an AFAD suka ba su masauki a otal kafin kai su garuruwansu daga baya.
Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 12,300 a hare-haren da ta kai ta sama da ta kasa a Gaza tun bayan harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Hamas ta kai. Adadin wadanda suka mutu a hukumance na Isra'ila, a halin yanzu, ya kai kusan 1,200