Jama'a sun yi bikin tunawa da girgizar kasa na ranar 6 ga watan Fabrairu a Hatay  inda suka yi tattaki cikin shiru /Hoto: AA  

Turkiyya ta gudanar da jimamin tunawa da wadanda girgizar kasar ranar 6 ga watan Fabrairun 2023 ta shafa, wadda ya afku a kudancin kasar, inda ta yi sanadin mutuwar mutum 53,537 tare da jikkata wasu fiye da 107,000.

Girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.7 da 7.6 ta afku ne a larduna 11 na Turkiyya da suka haɗa da Adana da Adiyaman da Diyarbakir da Elazig da Hatay da Gaziantep da Kahramanmaras da Kilis da Malatya da Osmaniye da kuma Sanliurfa.

Sama da mutane miliyan 14 ne girgizar kasar ta shafa a Turkiyya, da kuma wasu da dama a Syria.

'Silent March' in Hatay, commemorating those who lost their lives in February 6 earthquakes. /Photo: AA

Mutane a faɗin ƙasar ciki har da na yankunan da aka yi girgizar ƙasar, sun gudanar da tarukan jimamin don tunawa da wadanda suka mutu a bala'in.

An yi shiru na ɗan lokaci da misali ƙarfe 4.17 na asubahin ƙasar, daidai lokacin da masifar ta faru.

'Ifti'la'i na karni'

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi alkawari a ranar Talata cewa zai warkar da radadin ciwon wadanda girgizar kasar ta shafa.

"Zafin rayukan da muka rasa a girgizar kasa a tsakiyar Kahramanmaras da aka fuskanta shekara daya da ta wuce yana ci gaba da kona zukatanmu kamar ranar farko," a cewar sakon da Erdogan ya wallafa a shafin X.

Ya kuma jaddada cewa Turkiyya ta hada kai don yakar 'ifti'la'in Karni,' "Irin wadannan manyan bala'o'i da radadinsu sun zama gabar da aka jarabci hadin kanmu da hakuri da juriyarmu da 'yan uwantakar al'ummominmu.''

Mutane sun tuna da waɗanda suka mutu ta hanyar ziyartar kaburburansu a Kahramanmaras. /Hoto: AA

Erdogan ya kuma ce gwamnati na aiki tukuru don cika alkawuran da ta yi wa al'ummar kasar, inda ya kara da cewa: "Za mu ci gaba da wannan kokari har sai mun gina da kuma farfado da garuruwanmu."

Nan gaba a yau Talata shugaban zai halarci wani taro a Kahramanmaras na bai wa waɗanda suka tsira sabbin gidajen zama.

Shi ma Ministan Harkokin Wajen Hakan Fidan ya yi taron jimamin tunawa da girizar ƙasar da waɗanda suka rasa rayukansu.

Mutane sun yi tuni da wadanda girgizar kasar ta shafa a masallacin Igdir  ta hanyar yi  musu addu'o'i. /Hoto: AA

Ya rubuta a shafin X cewa "Za mu ci gaba da tsayawa da ƴan ƙsarmu," tare da gode wa ƙasashen da suka tsaya da Turkiyya a lokutan da ta fuskanci wahala.

Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya tunatar a ranar Talata cewa girgizar kasar ta haifar da radadin da ba za a iya misaltawa ba a zukatan al'ummar Turkiyya, ya kuma kara da cewa yana tunawa da daukacin mutanen 53,537 da suka rasa rayukansu.

“Allah ya kare mana al’ummarmu mai daraja da kyakkyawar kasarmu daga dukkan masifu da hadari,” kamar yadda ya rubuta a shafin X.

Masu hakar ma'adinai daga Zonguldak, wadanda suka shiga aikin agaji da ceto a yankin da girgizar kasa ta shafa a yankin Kahramanmaras, sun girmama wadanda suka mutu ta hanyar  addu'a. / Hoto: AA

An gina sabbin gidaje ga wadanda girgizar kasa ta shafa

Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta shirya wani rangadi a yankin da girgizar kasar ta shafa a Adiyaman ga 'yan jarida 45 na kasa da kasa.

Hotunan gine-ginen  da suka rushe a ifti'la'in girgizar kasar /Hoto: AA

Gwamna Osman Varol ya ba da bayanai game da kokarin da ake yi a birnin ga kungiyar 'yan jaridun kasashen waje 33 da 12 na Turkiyya.

Adiyaman na daya daga cikin larduna 11 da ke kudancin Turkiyya da girgizar kasar ta afku a ranar 6 ga watan Fabrairu.

Hotunan gine'ginen da girgizar kasar ya lalata. /Hoto: AA

“Mun yi asarar ‘yan kasarmu 8,387 a garin Adiyaman, kuma ina mika ta’aziyyata ga al’ummar yankin. Idan muka duba irin gine-ginen da aka yi a lardinmu, za mu ga jimillar gine-ginen sun kai 115,067, kuma adadin gine-gine masu zaman kansu ya kai 269,116 a cikin wadannan gine-gine."

Hotunan sabbin gidajen da aka gina a yankunan da girgizar kasar ta shafa. /Hoto: AA

"A cikin girgizar kasa, an ƙaddara cewa gine-gine 33,112 a cikin birnin 'sun rushe,' 'za a rushe su cikin gaggawa,' 'saboda sun lalace sosai,' wasu kuma 'lalacewar ba ta yi muni ba'," in ji shi.

Dan jaridar kasar Italiya Giuseppe Didonna ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa, sun ziyarci gidajen da aka gina wa wadanda girgizar kasar ta shafa.

Hotunan sabbin gidajen da aka gina a yankunan da girgizar kasar ta shafa. /Hoto: AA

Didonna ya ce: "Da fatan kowa zai koma rayuwarsa ta yau da kullun. An yi aiki mai kyau cikin sauri."

"Na zo yankin Indere a watan Satumban da ya gabata, a lokacin harsashin ginin kawai aka aza. Yanzu gine-ginen sun yi nisa, kuma na yi mamaki; aikin yana tafiya da sauri," in ji shi.

Hotunan sabbin gidajen da aka gina a yankunan da girgizar kasar ta shafa. /Hoto: AA

Ya kara da cewa: "Ina taya wadanda suka ba da gudunmawar murna, a ciki, akwai duk wani wurin da za a biya bukatun jama'a."

Hotunan sabbin gidajen da aka gina a yankunan da girgizar kasar ta shafa. /Hoto: AA
TRT World