Majalisar dokokin Turkiyya ta zabi Numan Kurtulmus, mataimakin shugaban Jam’iyyar AK a matsayin shugabanta na 30.
A zagaye na uku ana bukatar kuri’a 301 ne don lashe zaben.
An haifi Numan Kurtulmus, sananne a siyasar Turkiyya a gundumar Unye da ke lardin Ordu a 1959.
Kurtulmus ya shiga harkokin siyasa a 1998, a lokacin da ya zama shugaban jam’iyyar Refah a lardin Istanbul, daga baya ya zama mamban Hukumar Kula da Gudanarwa.
A 2008 ya zama shugaban Jam’yyar Fazilet, daga baya kuma ya kafa Jam’yyar Has a ranar 1 ga Nuwamban 2010. Bayan shekaru biyu da hakan kuma ya koma Jam’iyyar AKP.
A 2014, ya zama mataimakin firaministan Turkiyya a gwamnati ta 62.
A rayuwarsa ta Siyasa, Kurtulmus ya zama mataimakin firaminista a gwamnati ta 42 inda ya zama kakakin gwamnatoci na 63 da 64 da kuma 45.
Ya kuma rike mukaminin ministan raya al’adu da yawon bude ido a lokacin da aka yi kwaskwarima ga majalisar ministocin gwamnati ta 65.
Kurtulmus ya ci gaba da zama mai fada a ji a Jam’yyar AKP, saboda kasancewar sa daya daga cikin ‘yan kwamitin zartarwar jam’iyyar a yayin babban taronta karo na 6.
A yanzu shi ke rike da mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar AKP.
Yadda majalisar ke zabar shugaba
'Yan takara bakwai ne suka fafata a zaben, cikin har da Kurtulmus, dan takarar hadin gwiwa na AKP da MHP; Tekin Bingol na CHP, Tulay Hamitogullari Oruc ta jam’yyar YSP, Mustafa Cihan Pacaci na jam’yyar IYI, Mustafa Yeneroglu na DEVA da kuma Serap Yazici Ozbudun na hadin gwiwar jam’iyyaun Gelecek da Saadet.
Kundin tsarin mulkin Turkiyya ya tanadi cewar ana zabar shugaban majalisar dokoki ta hanyar jefa kuri’a a sirrance har a matakai hudu a rana guda.
A zagaye biyu na farko dole wanda zai yi nasara ya samu kaso biyu cikin uku na yawan ‘yan majalisar wato kuri’a 400 kenan.
Idan aka tafi zagaye na uku kuma, to ana son dan takara ya samu kuri’a 301 ne don zama shugaban majalisar dokokin.
Idan har a wannan zagaye na uku ma ba a samu wanda ya yi nasara ba, to ‘yan takar biyu da suka samu mafi yawan kuri’a za su fafata a zagaye na hudu, kuma duk wanda ya haura dayan da kuri’a ko guda daya ce shi ne ya yi nasara.
A zaben 14 ga Mayu, Jam’iyyar AK ta samu kujera 268 a majalisar dokoki.
Jam’yyar MHP kuma ta samu kujera 50, Refa kuma na da kujera shida, wanda hakan ya sanya Kawancen Al’umma yake da kujera 323 a majalisar.
Kawancen Kasa na manyan ‘yan hamayya kuma na da kujera 212 a majalisar dokokin.
Kawancen Leba da “Yanci ne ya samu sauran kujeru 65 na majalisar, wanda ya hada da kujeru 61 na YSP da 4 na Jam’yyar Leba ta Turkiyya.