Ankara za ta karɓi baƙuncin wasu daga cikin fursunoni Falasɗinawa da Isra'ila ta saka a wani yunƙuri da take yi na bayar da gudunmawarta ga yarjejeniyar tsagaita ta Gaza, kamar yadda Fadar Shugaban Turkiyya ta sanar a wata sanarwa da ta fitar.
Sanarwar da aka fitar a ranar Talata ta bayyana cewa Shugaba Recep Tayyip Erdogan ne da kansa ya umarci Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Turkiyya kan ta shirya yadda fursunoni 15 na Falasɗinawa da Isra'ilar ta saki zuwa Turkiyya a mataki na farko na yarjejeniyar.
A ɗaya daga sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wutar da Isra'ila ta gindaya ta ƙunsa, ta buƙaci Falasɗinawan da ta yanke wa hukuncin zama har abada a gidan yari ta kuma sake su a yanzu da su bar Falasɗinu har abada.
Hukumomin Turkiyya sun yi shirin karɓar wasu daga cikin wadannan fursunonin Falasdinawa, in ji sanarwar a hukumance.
Isra'ila da Hamas sun amince da tsagaita bude wuta, wadda ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu bayan an sha ƙoƙarin yin hakan a baya ba tare da samun nasara ba. Musayar fursunonin ta kasance ɗaya daga cikin batutuwa masu rikitarwa yayin tattaunawar.
Isra'ila ta ɗaure tare da tsare dubban Falasdinawa da ta kwashe a lokacin hare-haren soji a Gaza da aka yi wa kawanya da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye.
Tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023, Isra'ila ta kashe Falasdinawa kusan 50,000 tare da jikkata fiye da mutane 100,000 a yakin da ta ke yi na kisan kare dangi a Gaza bayan da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta kai wa Isra'ila hari tare da kame daruruwan mutane.
Bisa yarjejeniyar, Hamas za ta saki fursunonin sannu a hankali, sannan Isra'ila, a madadinta, za ta kubutar da dubban Falasdinawa daga gidajen yarin da take da su.
Wasu kasashe da dama kuma za su karbi bakuncin fursunonin Falasdinu.