Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa kasarsa za ta yi duk mai yiwuwa domin kare kasar daga kungiyoyin ‘yan ta’adda.
“Ba za mu bayar da kai bori ya hau ba ga mutanen da ke kai mana hare-haren ta'addanci. Ba za mu yi shakkar yin duk wani abu da ya dace ba game da tsaron Turkiyya,” kamar yadda Erdogan ya shaida wa taron jama’a a gabannin taron Jam’iyyar AK na musamman karo na hudu a Ankara a ranar Asabar.
A ‘yan kwanakin nan Turkiyya na ta gudanar da hare-hare ta sama a arewacin Syria da Iraki domin dakile hare-haren ta’addanci kan ‘yan kasar Turkiyya da dakarun kasar, ta hanyar “kawar da” ‘yan PKK/YPG da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda domin tabbatar da tsaron kan iyaka.
Wannan yunkurin yana zuwa ne bayan harin ta’addancin da aka dakile a ranar Lahadi a Ankara babban birnin kasar, inda wani mai harin ta’addanci ya yi kunar bakin wake a gaban ofishin Ma’aikatar Cikin Gida, inda dayan dan ta’addan kuma aka kama shi a gaban kofar shiga ma’aikatar.
An raunata ‘yan sanda biyu a harin da aka kai a ranar 1 ga watan Oktoba. Ma’aikatar Cikin Gida ta Turkiyya ta tabbatar da cewa maharan na da alaka da kungiyar ‘yan ta’adda ta PKK.
An kawar da mayakan PKK/YPG 14
Ma’aikatar tsaron Turkiyya a ranar Asabar ta bayyana cewa jami’an taron kasar sun “kawar da” akalla mayakan YPG/PKK 14 a arewacin Syria.
Turkiyya ta ce ta kai hare-hare a wasu yankuna a ranar Juma’a da dare. Hukumomin Turkiyya suna amfani da kalmar “kawar da” domin bayyana ‘yan ta’addan da ake magana a kai ko dai sun yi saranda ko an kashe su ko kuma an kama su.
Tun daga 2016, Ankara ta kaddamar da hare-hare da dama wadanda ta ci nasara kan kungiyoyin ‘yan ta’adda kan iyakokinta da Syria domin guje wa taruwar ‘yan ta’adda.
A yakin da Turkiyya take yi da ta’addanci tsawon shekaru 35, kasashen Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana kungiyar PKK a matsayin ta ta’addanci wadda ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 40,000, ciki har da mata da yara.
Kungiyar YPG ya kasance wani reshe ne na PKK da ke Syria.