Turkiyya za ta ci gaba da tona asirin Isra'ila kan abubuwan da ke faruwa a Gaza - Shugaba Erdogan

Turkiyya za ta ci gaba da tona asirin Isra'ila kan abubuwan da ke faruwa a Gaza - Shugaba Erdogan

Erdogan ya ce gwagwarmayar Hamas ta kwanaki 471 ta sake nuna ƙarara  juriya da kuma jajircewar da aka yi.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da tawagar ƙungiyar Hamas a birnin Ankara ciki har da Muhammad Darwish shugaban majalisar shura ta Hamas. / Hoto: AA      

Turkiyya za ta ci gaba da tona asirin Isra'ila kan abubuwan da ke faruwa a Gaza, a cewar shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan, yana mai bayyana fatansa na ganin nasara wajen kammala mataki na 2 da na 3 a yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma tsakanin Isra'ila da Hamas.

A ranar Labara ne dai Shugaba Erdogan ya gana da wata tawaga ta Hamas a fadar shugaban ƙasa da ke Ankara, ciki har da Muhammad Darwish, shugaban majalisar shura ta ƙungiyar.

Erdogan ya bayyana cewa, gwagwarmayar Hamas ta kwanaki 471 ta sake nuna ƙarara juriya da kuma jajircewar da aka yi.

Kazalika Shugaban ya jaddada cewa, Turkiyya za ta ci gaba da tofa albarkacin bakinta game da abubuwan da ke faruwa a zahiri a Gaza tare da bayar da tallafi.

Taron ya kuma samu halartar manyan jami'an Turkiyya da suka haɗa da ministan harkokin wajen ƙasar Hakan Fidan da shugaban hukumar leken asiri ta ƙasa (MIT) Ibrahim Kalin, da kuma shugaban sashen sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun.

TRT World