Rasha ta ce ba za ta kara wa'adin yarjejeniyar fitar da hasti ta tekun Bahar Maliya ba./ Hoto: AA

Turkiyya za ta ci gaba da gagarumin kokari da ayyukan diflomasiyya don ganin an dawo da yarjejeniyar fitar da hatsi ta tekun Bahar Aswad, in ji Shugaba Recep Tayyip Erdogan yayin tattaunawa da takwaransa na Rasha Putin.

A tattaunawa ta wayar tarho da Erdogan ya yi da Putin a ranar Larabar nan, shugabannin biyu sun amince cewa shugaban Rasha zai ziyarci Turkiyya, in ji sanarwar da Ma'ikatar Sadarwa ta Turkiyya ya fitar.

Da yake zayyana muhimmancin yarjejeniyar safarar hatsi ta Bahar Aswad a matsayin 'hanyar zaman lafiya’, Shugaba Erdogan ya kuma ce a lokacin da ake rikicin Rasha da Ukraine, bai kamata a dauki matakin da zai ta’azzara lamarin ba.

Erdogan ya ce dakatar da safarar hatsin na lokaci mai tsayi ba zai amfani kowa ba, inda ya kara da cewa kasashe matalauta da suka fi bukatar hatsin za su shiga halin kaka-ni-ka-yi.

Ya jaddada cewa farashin hatsi da ya sauko da kashi 23 a lokacin da yarjejeniyar ke aiki, ya karu da kaso 15 a makonni biyu da suka gabata.

A ranar 17 ga Yuli, Rasha ta dakatar da yarjejeniyar, wadda ta sanya hannu a kai a watan Yulin bara tare da Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya da Ukraine don dawo da safarar hatsi daga Ukraine tare da bi da shi ta Bahar Aswad wanda aka dakatar bayan fara rikicin kasashen biyu a watan Fabrairu.

Duk da kara wa'adin da aka yi a watan da ya gabata, Rasha ta yi korafin cewa ba a aiwatar da bangarenta na yarjejeniyar.

Shugaba Erdogan ya kuma gode wa Putin bisa aikawa da jiragen sama masu sauka a teku guda biyu don taya Turkiyya aikin kashe gobarar daji da ta kama a kasar.

Ya bayyana jin dadinsa kan yawan 'yan yawon bude ido na Rasha da suke kara nuna sha'awar zuwa Turkiyya, inda ya kara da cewar suna fatan a wannan shekarar ma za a kafa tarihi wajen samun maziyarta daga Rasha zuwa Turkiyya.

Tattaunawar zaman lafiya ta nan gaba

A karshen makon nan ne babban mashawarcin Shugaba Erdogan, Akif Cagatay Kilic zai halarci taron tattaunawar zaman lafiya na Ukraine da Saudiyya za ta karbi bakunci.

A yayin taron da za a yi ranar Asabar za a tattauna kan halin da ake ciki a Ukraine, za a kuma yi musayar ra'ayi don neman samar da zaman lafiya tsakaninta da Rasha.

Ana sa ran wakilan kawancen tsaro ta NATO da Hukumar Tarayyar Turai da Majalisar Tarayyar Turai da masu bayar da shawara kan sha'anin tsaron na kasashen Brazil da Canada da Denmark da Faransa da Jamus da Indiya da Italiya da Ukraine da Saudiyya da Afirka ta Kudu da Ingila da Amurka da Japan da Sweden da Denmark da Finland za su halarci taron.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce Moscow za ta sanya idanu da bibiyar taron da ma sakamakon da zai haifar.

Peskov ya ce "Babu tantama Rasha za ta sanya idanu kan wannan taro. Za mu so mu san wadanne irin manufofi ne ake shiryawa. Mun sha nanata cewa duk wani yunkuri da zai nemi a kawo zaman lafiya, to ya cancanci a girmama shi."

Kilic zai kuma halarci taron tattaunawa da takwarorinsa yayin babban taron.

Ana yabon Turkiyya a fagen kasa da kasa saboda rawar da take takawa wajen shawo kan rikicin Ukraine da Rasha, kuma ta sha yin kira ga kasashen biyu da su kawo karshen wannan rikici.

TRT World