Shugaban Turkiyya ya bayyana a ranar Asabar cewa ƙasarsa za ta gudanar da aikinta na tsaron sararin samaniyar "Steel Dome" (Rumfar Ƙarfe).
"Muna fata za mu gudanar da aikinmu na 'Steel Dome' (Rumfar Ƙarfe) da duka abin da ya ƙunsa. Idan su (Isra'ila) suna da Iron Dome, mu ma za mu yi Steel Dome," kamar yadda Recep Tayyip Erdogan ya faɗa a wajen Bikin Ƙaddamarwa da Miƙa Tuta a Kwalejin Yaƙi ta Sama.
Steel Dome zai tabbatar da cewa matakanmu na tsarin kariya ta sama da duka na'urorinmu masu gano motsi da makamai suna aiki tare da juna," a cewar Erdogan.
Erdogan ya jaddada ƙara shaharar Turkiyya a ɓangaren fasahar jirage marasa matuƙa.
"Ana sa ido da ƙyashi kan nasarar da muka cim ma a ɓangaren jirage marasa matuƙa, ba wai kawai daga ƙasashe abokanmu da 'yan'uwanmu ba, har ma daga ko ina a duniya," a cewarsa.
Idan aka ƙaddamar da jirage marasa matuƙa na Kizilelma and ANKA-3, waɗanda ake ci gaba da gwada su, Turkiyya za ta zama wacce ake damawa da ita a wani "sabon rukuni" a wannan ɓangaren, kamar yadda Erdogan ya bayyana.
Yaƙi da Ta'addanci
Shugaban na Turkiyya ya kuma nanata aniyar Turkiyya ta inganta ƙarfinta na soji, yana mai cewa: "Muna ƙoƙarin ƙerawa da bunƙasawa ko kuma sayo duk wani abu da rundunar sojin samanmu ke buƙata, tun daga makamai masu linzami zuwa na'urorin kariya ta sama."
“Rundunar sojin samanmu na sauke nauyin da ya rataya a wuyanta wajen kawar da barazana ga tsaron ƙasarmu, musamman a yaƙi da ta’addanci,” inji shi.
Da yake magana game da ci gaba da Operation Claw-Lock, wanda aka ƙaddamar a shekarar 2022 don kai hari kan maɓoyar 'yan ta'addar PKK a arewacin Iraƙi, Erdogan ya ce za su tabbatar da cewa 'yan awaren sun daina zama wata barazana ga "al'ummarmu da 'yan uwanmu na Iraƙi."
Erdogan ya ce wasu ƙawayen, maimakon goyon bayan Turkiyya, ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen nuna goyon bayansu ga ƙungiyar ta'addanci ta PKK a Siriya da kuma kyakkyawar maraba ga jagororin ƙungiyar ta'addanci ta 'yan aware.
Ya ƙara da cewa "Muna dogara ne kawai da karfinmu da jajircewarmu."
Erdogan ya kuma yaba wa dakarun Turkiyya dangane da shawo kan ƙalubalen da suka fuskanta da suka haɗa da juyin mulkin da ƙungiyar ta'addanci ta Fetullah ta shirya a shekarar 2016.
"Ba wai kawai mun tumɓuke ƙungiyar ta'addanci ta FETO da ta yi girma kamar muguwar cuta sankara kusan shekaru 40 ba, mun kuma ƙarfafa sojojin mu a kowane fanni," in ji shi.
Shugaban ya ce Turkiyya na haɗin kai da "abokanta da 'yan uwanta a duk inda ake buƙata."
Ankara na goyon bayan ƙawayenta a Libya da Somalia da Azarbaijan. Shugaban ya ce babu wani soja a duniya, in ban da rundunar sojan Turkiyya, da za ta iya samun irin wannan nasarar fiye da iyakokinta cikin ƙanƙanin lokaci.