Masu shigar da ƙara na Turkiyya sun ƙaddamar da wani bincike a kan wani harin sama na Isra'ila da ya kashe 'yan ƙasar Turkiyya uku waɗanda suke ƙoƙrin tsallakawa daga Lebanon zuwa Isra'ila, a cewar jami'ai.
Masu shigar da ƙara a babban birnin ƙasar Ankara a ranar Laraba sun ce sun buɗe bincike a kan lamarin.
An kai gawarwakin mutanen zuwa Turkiyya sannan ana gudanar da bincike a kansu, a cewar sanarwar.
Idan aka kammala binciken, za a aika muhimman bayanan zuwa ofishin babban mai shigar da ƙara, sanarwar ta ƙara da cewa.
Tun watan da ya gabata ne ba a ga mutanen ba
A cikin kwanaki, Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyyan ta fitar da sanarwa tana yin Allah wadai da kakkausar murya kan "wannan harin na take doka da ya jawo mutuwar 'yan ƙasarmu."
Ta ce: "An gano cewa 'yan ƙasar Turkiyya uku, waɗanda aka neme su aka rasa a lokacin da suka yi ƙoƙarin shiga Isra'ila daga Lebanon, sun rasa rayukansu sakamakon wani harin sama da Isra'ila ta kai yankin.