Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya yi Allah wadai da cin zarafin 'yan jaridar TRT a yayin da suke gabatar da rahoto kai tsaye a Tel Aviv.
Altun ya jaddada cewa hukumomi da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna na kai hari ga 'yan jaridar da ke fallasa yadda rikicin yankin ke wakana.
“’Yan jaridar da ke shaida wa duniya kisan kiyashin da ake yi a Gaza da Lebanon, ba wai jami’an tsaron Isra’ila ne kadai ke kai musu hari ba, har ma da ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila da ke ɓad-da-kama a matsayin fararen hula,” in ji Altun a wata sanarwa da ya fitar ta shafin X bayan aukuwar lamarin.
Lamarin dai ya hada da ɗan jaridar TRT Mucahit Aydemir da mai daukar bidiyo Omar Awwad, wadanda wani dan Isra'ila ya katse musu aiki, da alama farar hula ne ya tarwatsa su, yayin da suke ba da rahoto kan barnar da makamai masu linzami suka yi a Tel Aviv.
Duk da gabatar da takardun shaidar aikin jarida, sai da aka tsangwame su, inda mutumin ya ce musu "ku tafi ku yi aikinku a Turkiyya."
Altun ya jaddada cewa, wannan lamari ne da ya fara wuce gona da iri, inda ya yi nuni da wani salon cikas da nufin dakile yadda ayyukan Isra'ila ke yi a Gaza da Lebanon. "Sojojin Isra'ila da fararen hula suna kai hari ga 'yan jaridar da ke bayyana tashin hankalin da ke faruwa," in ji shi.
"Ga wadanda suke tunanin za su iya boye gaskiya ta hanyar kokarin hana 'yan jarida yada labaran abubuwan da ke faruwa a duniya: ba za ku yi nasara ba," in ji Darakta Janar Mehmet Zahid Sobaci na TRT yayin da yake Allah wadai da lamarin.
'Rashin hankali tuburan'
Wannan tsokanar ta dauki wani yanayi mai matukar tayar da hankali lokacin da ‘yan sandan Isra’ila suka tsare ‘yan jaridar TRT, ba wai wanda ya tayar da hankali ba, lamarin da ya sa Altun ya bayyana abin a matsayin “rashin hankali tuburan.”
Altun ya jaddada cewa, "yadda 'yan sandan Isra'ila suka tsare ma'aikatan TRT ba wai masu tayar da hankali ba tare da sake gudanar da bincike ya nuna cewa Isra'ila na cikin hauka muraran.
Shugaban sashen sadarwar ya bayyana cewa, wannan cin zarafi ba lamari ne da za a yi wasarere da shi ba, yana mai nuni da cewa jami'an tsaron Isra'ila da fararen hula suna kai hari kan 'yan jaridun da ke fallasa tashin hankalin da Tel Aviv ke ci gaba da yi a Zirin Gaza da Lebanon.
Ya sha alwashin cewa, duk da kokarin dakile ayyukansu, 'yan jaridun Turkiyya za su ci gaba da bayar da rahotanni kan gaskiyar rikicin, tare da tabbatar da an sanar da duniya irin ayyukan da Isra'ila ke yi a Gaza da Lebanon.