Turkiyya ta bayyana cikakken goyon baya ga Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kula da Falasdinawa 'Yan Gudun Hijira (UNRWA),
Da yake bayani a wajen Taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, ciki har da batun Falasdinu, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Ahmet Yildiz a ranar Laraba ya nuna yabawarsa ga Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini saboda "kokarinsa na cika dukkan ayyukan UNRWA duk da kalubalen da ake fuskanta".
Ya yi tsokacin cewa "Wahalar da ake sha a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ba za ta misaltu ba" Yildin ya jaddada cewa Yammacin Gabar Kogin Jordan da ke karkashin kawanya "na cikin babban rikicin 'yan asalin yankin da 'yan mamaya da kuma zaluncin da Isra'ila ke ci gaba yi wa Falasdinawa."
Ana ci gaba da samar da sabbin unguwannin Yahudawa ba bisa ka'ida ba, ana rushe gidajen Falasdinawa, da fitar da su daga gidajensu da karfin tuwo da kwace filayensu. Ya tunatar da cewar daga 7 ga Oktoba zuwa yau an kama akalla Falasdinawa 7,000.
Matsananciyar wahala da ba a taba tsammata ba a Gaza
A zamanin yau Gaza ne yankin da ya fi kowanne fuskantar bala'in da dan'adam ya janyo. A kan idanuwanmu ana rushe gidaje da kashe rayukan da ba a taba tsammata ba. Abin bakin ciki ne, hakan na karya zukata," in ji Ahmet Yildiz
Ya yi karin haske ga yadda adadin wadanda aka kashe ya karu sosai, kuma jama'a na cikin hatsarin kamuwa da cutar yunwa.
"Ana karar da zamani gaba daya a cikin yaki, a cikin azzalumin tsarin kwace yankuna da talauta mutane," in ji shi.
Da yake tunatar da har yanzu ba a yi aiki da matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta dauka na a tsagaita wuta da kuma matakan farko na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ba, Yildiz ya ce "karara ana kin yin aiki da dokokin kasa da kasa".
Ma'aikatan MDD sama da 200 aka kashe a hare-haren Isra'ila
Ya ce "Duk da wahalhalun da ake fuskanta, UNRWA sun zama masu sanya farin ciki da fata nagari. Ga Falasdinawa, ga mu baki daya."
Ya kuma yi karin haske da cewa UNRWA da dukkan ma'aitanta sun sadaukar da kawunansu wajen raba kayan abinci, koyarwa da kula da lafiya. Ya tunatar da cewa an kashe sama da ma'aikatan MDD 200 a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila.
Ya kara da cewa "Duk da haka gwamnatin Isra'ila na ci gaba da yada sharri da bata suna don bakanta hukumar, duk da cewar dai ba a yarda da abin da take cewa ba."
Ya tunatar da cewa "Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya na yi wa UNRWA kallon wata hukuma ta wucin gadi, wadda ta fara aikinta a 1949 bayan korar Falasdinawa daga yankunansu."
Burin kafa kasashe biyu
Ya bayyana cewa UNRWA na nufin dawowar mutunci, yana mai kara wa da cewar "UNRWA na fada tabbas batun Falasdin na nan da dumi-duminsa."
Ya kuma zayyana cewa "UNRWA na da alhakin siyasa, doka, jinkai da kyawun hali na kasashen duniya, har zuwa lokacin da za a tabbatar da burin kafa kasashe biyu."
Da yake bayyana cikakken goyon bayan Turkyya ga UNRWA, ya yi kira ga kasashe mambobin MDD da su ci gaba da ayyukansu."
Ya kara da cewa "Turkiyya a matsayinta na shugaban kwamitin ayyukan samar da kudade ga UNRWA kuma bayar da gudunmowa a koyaushe, za ta ci gaba da bayar da gudunmawa ga ayyukan hukumar."