Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da shugaban majalisar mulkin Sudan Abdel Fattah al-Burhan sun gana a fadar shugaban kasar Turkiyya a Ankara a ranar 06 ga Mayu, 2024. / Hoto: AA  

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da shugaban majalisar mulkin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, sun tattauna a ranar Juma'ar nan kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, tare da batutuwan da suka shafi yankunan da na duniya baki ɗaya.

A tattaunawar ta wayar tarho, Erdogan ya bayyana yadda sulhun rikicin da Ankara ta yi tsakanin Somaliya da Habasha ya yi tasiri sosai wajen samar da zaman lafiya a yankin, in ji sanarwar da Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta fitar.

Kazalika Erdogan ya ce, Turkiyya za ta iya shiga tsakani wajen warware takaddamar da ke tsakanin Sudan da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Shugaban ya bayyana muhimman manufofin Turkiyya na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sudan, da kuma kare iyakoki da 'yancinta, tare da hana kasar zama yanki da ke tsoma baki kan lamuran kasashen waje. .

Ci gaban yankin

Da yake zantawa kan ci gaban yankin da Burhan, Erdogan ya ce bayan shekaru 13 na rikicin jinƙai da yakin basasa, al'ummar Siriya sun kai wani mataki na yanke shawara kan makomarsu, yana mai jaddada cewa Turkiyya za ta ba da gudummawa ga wannan tsari.

Turkiyya tana bayan haɗin kan siyasar Siriya da kuma 'yancin yankunan kasar, kuma wannan goyon bayan zai ci gaba da tabbatar da cewa gwamnatin rikon ƙwarya a Siriya ta ɗauki cikakkun matakai na bai daya, tare da yi wa al'ummar ƙasar hidima, ba tare da haifar da wata barazana ga makwabtanta ba, in ji shugaban.

Sudan ta fada cikin rikici tsakanin rundunar sojojin ƙasar da dakarun sa- kai na RSF tun daga watan Afrilun 2023.

Rikicin dai ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20,000 tare da raba sama da mutum miliyan 14 da muhallansu, a cewar alkalumman Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin yankin.

AA