Shugaba Erdogan ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. / Hoto: AA

Turkiyya za ta yi zaman makoki na kwana guda a ranar Larabar nan sakamakon gobarar da ta kama a wani otel a lardin Bolu inda aƙalla mutane 76 suka rasa rayukansu, in ji shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Shugaban ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu da fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata. Ya tabbatarwa da jama'a cewa za a hukunta waɗanda ke da alhakin afkuwar gobarar saboda sakaci ko rashin ɗa'a.

“Lokaci ne na goyon baya, haɗin-kai, da tausayi - ba na muhawarar siyasa ba," in ji Erdogan, yana mai kira ga dukkan ɓangarori, ciki har da 'yan siyasa, kafafen yaɗa labarai, da mahukunta, da su nuna damuwa ga mawuyacin halin da ƙasar ta shiga.

Shugaban ƙasar ya ƙarƙare da fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata da haƙuri ga 'yan'uwan waɗanda suka mutu a gobarar, inda ya kuma bayyana fatan za a kawar da sake afkuwar irin wannan ibtila'i a Turkiyya a nan gaba.

Gobara ta kama a otel mai hawa 12 a wajen wasa a dusar ƙanƙara da ke arewa maso-yammacin Turkiyya a ranar Talata, inda aƙalla mutane 76 suka rasa rayukansu, in ji mahukunta.

Aƙalla wasu mutanen 51 sun jikkata a otel din Grand Kartal da ke Kartalkaya, a tsaunukan Koroglu na Bolu, nisan kilomita 300 gabas da Istanbul.

Tsagaita wuta a Gaza, Syria

Game da Syria, Erdogan ya yi kira ga Larabawa da duniyar Musulunci da su taimaka wajen farfaɗowar Syria "kafin wasu", Ƙasashen Yamma su janye takunkuman da suka sanya wa ƙasar da yaƙi ya tagayyara.

Jawabin nasa ya zo ne bayan kammala zaman majalisar zartarwa a Ankara a ranar Talata.

Game da tsagaita wuta a Gaza, Erdogan ya ce hotunan musayar fursunoni sun bayyana wane ne ya san darajar ɗan'adam, inda ya kuma soki Isra'ila.

Ya ƙara da cewa "'Yan'uwanmu maza da mata a Gaza sun shan wahala, amma ba su miƙa kai bori ya hau ba."

Turkiyya za ta hanzarta dukkan ƙoƙari don samar da zaman lafiya madauwami a yankin, "kuma tsagaita wutar dama ce mai muhimmanci" a Gaza, in ji shugaba Erdogan.

TRT World