Mutane miliyan 62.2 ne suka ziyarci Turkiyya a shekarar 2024, ƙarin kashi 9 cikin 100 aka samu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata./ Hoto: AA     

Kudaɗen shigar da Turkiyya ta samu daga fannin yawon buɗe ido a shekarar 2024 ya kai dala biliyan 6.1, wato ƙarin kashi 8.3 cikin ɗari, adadin da ya kafa tarihi idan aka kwatanta da abin da ƙasar ke samu a duk shekara.

Ƙasar dai na ci gaba da ƙarfafa fannin, inda take ƙara samun masu zuwa ziyara daga ƙasashen duniya a kowace shekara.

A shekarar 2024, mutane miliyan 62.2 ne suka kai ziyara Turkiyya, adadin da ya ƙaru da kashi 9 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, wanda ya zarta yawan masu yawon bude ido miliyan 49.2 da aka samu a shekarar 2023, kamar yadda Hukumar Ƙididdiga ta Turkiyya ta bayyan.

Matsakaicin ƙudin da kowane baƙo ɗaya da ya shiga ƙasar a shekarar 2024 ya kashe ya kai dala 972, kana dala 97 a kowace rana.

A 2024, mafi yawancin baƙin da suka kawo ziyara Turkiyya sun zo ne don nishaɗi da wasanni da kuma ayyukan al'adu, kashi 64.9 na jimillar adadin da aka samu.

Daidaitaccen haɓakan tattalin arziki

A wani saƙo da ya wallafa a kafofin sada zumunta kan kuɗaɗen da Turkiyya take samu daga ɓangaren yawon buɗe ido, Mataimakin Shugaban Turkiyya Cevdet Yilmaz ya bayyana cewa, "Kuɗin da muka samu a ɓangaren yawon buɗe ido ya zarce abin da muka yi tunanin samu a Shirinmu na Matsakaicin Zango, inda ya kai abin da bai taɓa kai wa ba, dala biliyan $61.1." Ya kuma jaddada cewa yawan masu yawon buɗe ido da suka shigo ƙasar ya ƙaru fiye da abin da aka yi tsammani.

Yilmaz ya bayyana cewa wannan gagarumin haɓakan da fannin na yawon buɗe ido ya yi ya ƙara bunƙasa harkokin tattalin arziki ya kuma ba da gudumawa wajen daidaita haɓakar tattalin arziki.

"Ya samar wa mutane da yawa damammakin ayyukan yi, musamman matasa, sannan ya taka muhimmiyar rawa wajen cike giɓin kuɗade ta hanyar kawo kuɗaɗen ƙasashen waje cikin ƙasarmu," kamar yadda ya bayyana.

Ya kuma bayyana cewa wannan tasirin ya ƙarfafa manufofin Turkiyya wajen daidaita al'amura da kuma bunƙasar ɓangarori daban-daban.

Da yake hasashen 2025, lokacin da ake sa ran kuɗin da za a samu daga yawon buɗe ido zai kai dala biliyan 63.6, Yilmaz ya bayyana fatan za a ci gaba da samun wannan kyakkyawan tasiri.

TRT World