Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gana da mambobin Kungiyar Kasashen Musulmai (OIC) da Kungiyar Tuntuba Game da Gaza ta Gamayyar Kasashen Larabawa a Amman.
A yayin taron a ranar Laraba, mambobin sun tattauna kan kokarin dakatar da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza da ƙarfafa neman tsagaita wuta da kai kayan agajin gaggawa, da magance ci gaba da mamayar Yammacin Kogin Jordan da tsokanar fada game da matsayin Masallacin Kudus da Gabashin birni Kudus da ke karkashin mamaya.
"Kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Gaza tare da rikicin 'yan kama wuri zauna da ke zaluntar Falasdinawa, da ma hare-haren sojojin Isra'ila a Yammacin Kogin Jordan sun yi kamari. Dole ne kasashen duniya su dauki mataki na nan-take don dakatar da Isra'ila daga kai hare-hare, wanda ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankinmu da ma sauran kasashen duniya," in ji sanarwar da ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar bayan tattaunawar Fidan din.
Sanarwar ta kara da cewa "OIC da Kungiyar Tuntuba Kan Gaza ta Gamayyar Kasashen Larabawa za su ci gaba da kokarin da suke yi na ganin an tabbatar da kafa kashe biyu don kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Falasdinu, sannan da ganin kasashe da dama sun amince da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa da za ta zama Mamba a majalisar Dinkin Duniya."
Wannan ganawa ta biyo bayan taron Kungiyar a makon da ya gabata a Madrid, wanda ya hada da wakilai daga Sifaniya da Norway da Slovenia da Tarayyar Turai da sauran kasashe.
Kungiyar Tuntuba ta Gaza da mambobin OIC da Gamayyar Kasashen Larabawa suka kafa a wajen Taron Musamman na Hadin Gwiwa da suka yi a watan Nuwamban bara a Riyadh, na aikin diplomasiyya a fadin duniya don dakatar da hare-haren Isra'ila a Gaza.