Naɗe-Naɗen na zuwa ne wata guda bayan Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan ya miƙa sunayensu. / Hoto: TRT World

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep tayyip Erdogan ya naɗa sabbin jakadu zuwa Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka.

Saƙon da aka wallafa a jaridar gwamnatin Turkiyya a ranar Juma'a ta ce, an naɗa jakadan Turkiyya a Majalisar Ɗinkin Duniya Sedat Onal a matsayin sabon jakada a Amurka.

Ahmet Yildiz, Mataimakin Ministan Harkokin Waje kuma ya zama sabon jakadan Turkiyya a Majalisar Ɗinkin Duniya.

Sabbin jakadu zuwa Chile, Guinea, Vietnam da Guatemala.

Kazalika an naɗa Rifat Cem ornekol a matsayin jakadan Turkiyya a Guinea, inda Ahmet Ihsan kiziltan kuma aka tura shi Chile a matsayin jakadan Turkiyya.

Korhan Kemik ya zama jakadan Turkiyya a Vietnam, sai Beliz Celasin Rende da aka naɗa a matsayin jakadan Turkiyya a Guatemala.

Sauran waɗanda aka miƙa sunayensu don naɗa su a matsayin jakadu sun haɗa da Mehmet Salt Uyanik zuwa Bulgaria, Gokcen Kaya zuwa Costa Rica, Semih Lutfu Turgut zuwa Sri Lanka da Ahmet Ergin zuwa Equitorial Guinea.

TRT World