Ranar Alhamis Turkiyya ta tura jiragen soji biyar, ciki har da jirage biyu samfuran A400M, domin kwashe sauran 'yan kasar da ke Sudan. Hoto/AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya ce sun kwaso mutum 1,834 daga Sudan, ciki har da mutum 249 'yan kasashe19.

"Muna tuntubar kowanne dan kasarmu da ke son dawowa gida," in ji Mevlut Cavusoglu a hirarsa da TRT Haber ranar Juma'a.

Majiyoyin difilomasiyya na Turkiyya sun bayyana cewa Cavusoglu ya yi magana ta wayar tarho da Mohammed Hamdan Dagalo, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), inda suka tattauna game da kwashe Turkawa daga Sudan.

Ranar Alhamis Turkiyya ta tura jiragen soji biyar, ciki har da jirage biyu samfuran A400M, domin kwashe sauran 'yan kasar da ke Sudan.

Tun da farko ranar Juma'a, Ma'aikatar Tsaron Turkiyya ta sanar cewa an kai hari da kananan makamai kan jirgin kasar mai lamba C-130 a sansanin sojin sama na Wadi Seidna da ke Sudan.

Da yake magana game da hanyoyin shawo kan rikicin Sudan, Cavusoglu ya ce: "Mataimakin ministanmu (Burak Akcapar) zai tafi Sudan makon gobe don shiga tsakani."

Ranar Alhamis da daddare aka sake kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin sojin Sudan karkashin shugabancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da dakarun RSF da Janar Dagalo yake shugabanta.

Rikicin, wanda ya barke ranar 15 ga watan Afrilu, ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 460 yayin da sama da mutum 4,000 suka jikkata, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Sudan.

AA