Jami'an tsaron Turkiyya sun kawar da 'yan ta'addan PKK/YPG 17 a arewacin Iraƙi da da arewacin Syria, kamar yadda Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ta tabbatar.
Ma'aikatar ta bayar da rahoton cewa a ranar Lahadi an far wa 'yan ta'addan PKK 15 a yankunan Gara da Metina da kuma yankin arewacin Iraƙi.
Sauran 'yan ta'addan biyu na PKK/YPG an kai musu hari ne a yankin Manbij da ke arewacin Syria.
Ma'aikatar ta bayyana cewa sojojin Turkiyya za su ci gaba da aikinsu na yaƙi da 'yan ta'adda ba ƙaƙƙautawa a duk inda suke kamar yadda ma'aikatar ta bayyana.
Hukumomi a Turkiyya suna amfani da kalmar "kawarwa" domin nuna cewa ko dai 'yan ta'addan da ake magana a kan su an kama su ko kuma an kashe su
Aikin da Turkiyya ke yi na yaƙi da ta'addanci ya kusan kawar da 'yan ta'addan baki ɗaya a cikin ƙasar. A halin yanzu 'yan ta'addan na aiki ne daga kan iyakar ƙasar. Suna yawan ɓoyewa a arewacin Iraƙi kusa da iyakar Turkiyya, domin kitsa kai hari a Turkiyyar.
A 2022, Turkiyya ta ƙaddamar da rundunar Operation Claw-Lock domin kai hari kan maɓoyar 'yan ta'addan PKK a yankunan Metina da Zap da Avasin-Basyan da ke arewacin Iraƙi.
A tsawon shekara 40 da kungiyar ta yi tana ta'addanci a Turkiyya - kasar Turkiyya da Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai sun ayyana PKK a matsayin kungiyar ta'addanci wacce ke da alhakin mutuwar mutum kusan 40,000 da suka hada da mata da yara har da jarirai.