Cibiyar yaki da labaran karya ta gwamnatin Turkiyya ta karyata wasu labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa Isra'ila ta kai hari kan rumbunan gidaniyar ba da agaji ta Red Crescent ta Turkiyya tare da lalata wasu gine-gine mallakin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasar (AFAD).
A sanarwa da cibiyar ta fitar a ranar Litinin a shafinta na X, ta bayyana cewa ginin da ake magana a kai, wanda rahotanni suka bayyana cewa an barnata shi sosai sakamakon bama-bamai da Isra'ila ta harba wani dakin ajiyar kayayyakin jinƙai ne mallakin gidauniyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu da aka gina tare da taimakon kungiyar agaji ta Red Crescent ta Turkiyya.
"Ikrarin cewa "Isra'ila ta kai hari kan wuraren ajiyar kayayyakin agaji ta Red Crescent na Turkiyya da kuma haifar da ɓarna masu tarin yawa a wani ginin AFAD na kasar" da ke yawo a wasu shafukan sada zumunta ba gaskiya ba ne.
"Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Turkiyya ta taimaka wajen gina cibiyar Red Crescent ta Falasdinu kuma ba ta da wani takamaiman wuri a Gaza. Don Allah a yi watsi da zarge-zarge marasa tushe,” in ji sanarwar.
Tun karshen makon da ya gabata ne sojojin Isra'ila suka zafafa kai hare-harensu ta sama da ƙasa a Zirin Gaza, yanayin da ke zama na wuce gona da iri, tun bayan harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Adadin Falasdinawan da suka mutu kawo yanzu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta yi ta kai wa Gaza ya haura mutum 8,306, a cewar ma'aikatar lafiya ta yankin da aka yi wa ƙawanya a ranar Litinin.
''Adadin mutanen da suka mutu sun haɗa da yara 3,457 da mata 2,136, yayin da mutum sama da 21,048 suka jikkata, a cewar kakakin ma'aikatar Ashraf al Qudra yayin zantawarsa da manema labarai a birnin Gaza.
A daya bangare kuma akalla Isra’ilawa 1,538 ne suka mutu a rikicin.