Migrants

Jami’an tsaron Turkiyya sun kama jimillar bakin haure 261 a wasu farmakai da suka kai a fadin kasar.

Jami’an tsaron na Turkiyya sun fara cafke bakin haure Falasdinawa 20 a yankin Bodrum na lardin Mugla.

Haka zalika jami’an sun sake kama bakin haure 77 da suka hada da Falasdinawa da ‘yan Afganistan a cikin wani jirgin ruwan roba a tekun gundumar Ayvaik da ke lardin Canakkale.

A gefe guda kuma an sake samun wasu bakin hauren 113 a tsakiyar teku a lokacin da jami’an tsaron tekun Girka suka hankada su zuwa iyakar ruwan Turkiyya da ke gundumar Cesme a lardin Izmir, an kuma kama karin wasu 26 a dai wannan yanki.

A gabar Tekun Kusadasi kuma an kubutar da wasu bakin hauren 25 bayan da jami’an tsaron tekun Turkiyya suka hankada su zuwa iyakar ruwan Turkiyya.

An kai dukkan bakin hauren zuwa hedikwatar Hukumar Kula da Shige da Fice ta yankunan.

Turkiyya ta zama wata gada da ‘yan gudun hijira ke bi don isa ga kasashen Turai da manufar fara rayuwa mai inganci da samun walwala.

Turkiyya da kungiyoyin kasa da kasa sun soki halayyar Girka da ta saba ka’ida, inda suke kora ‘yan gudun hijira da suka samu a kan teku zuwa iyakar ruwan Turkiyya, wanda hakan ke barazana ga rayuka da dama.

TRT World