Fidan ya jaddada cikakken tsarin kasarsa na bunkasa dangantakar tattalin arziki da ci gaba, da ɓangaren kiwon lafiya da samar da abinci da kula da muhalli. / Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada aniyar kasarsa ta karfafa kawance da kasashen Afirka.

Ya jaddada hakan ne a taron bitar ministoci karo na uku na kawancen Turkiyya da Afirka a kasar Djibouti da ke gabashin Afirka a ranar Lahadi.

Ministan ya fara ne da isar da gaisuwar shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan tare da yaba wa shugabannin Tarayyar Afirka bisa gudunmawar da suka bayar wajen taron.

Ya kuma yi magana kan adadin matasan da Afirka ke da su da albarkatu masu yawa, da kasuwanni masu tasowa, wadanda ya lura za su kai nahiyar “babban matsayi” a ƙarni na 21.

Duk da haka, ya kuma bayyana irin kalubalen da Afirka ke fuskanta, wadanda suka hada da "ta'addanci, rashin daidaito, illolin sauyin yanayi, da rashin ci gaba da kuma yawaitar masu tafiya ci rani.”

Turkiyya, a matsayin abokiyar huldar Ƙungiyar Tarayyar Afirka tun daga shekarar 2008, ta yi kokarin raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ta hanyar da aka tsara da kuma nagartaccen tsari.

Fidan ya jaddada yadda Ankara ke sadaukarwa domin “samar da mafita ga matsalolin Afirka” yana mai tabbatar da matsayar Turkiyya da na ƙungiyar ta AU daidai da muradun 2063, na tabbatar da cewa an samu ci gaba mai kyau a faɗin nahiyar.

A yayin da yake magana kan matsalolin tsaro, Fidan ya jaddada goyon bayan Turkiyya ga kasashen Afirka wajen yaki da ta'addanci da samar da kwanciyar hankali a yankunan da tashe-tashen hankula suka shafa.

Ya mai da hankali musamman kan halin da ake ciki a Sudan, inda ya bukaci kasashen duniya da su hada kai don ganin an tsagaita bude wuta cikin gaggawa da kuma zaman lafiya mai dorewa.

Tun daga tsakiyar watan Afrilun 2023, sojojin Sudan da dakarun RSF suja soma wani ƙazamin yaƙi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20,000 tare da raba sama da mutane miliyan 10 da muhallansu, a cewar MDD.

Kasashen duniya da MDD na ta jaddada kira kan a kawo karshen tashe tashen hankula, yayin da rikicin ke barazanar jefa miliyoyin mutane cikin yunwa sakamakon karancin abinci a jihohi 13 cikin 18 na kasar Sudan.

Ta fuskar tattalin arziki, Fidan ya yi tsokaci kan yadda Turkiyya ta ƙara faɗaɗa kasuwanci da Afirka, wanda ya zarce dala biliyan 35 a shekarar 2023, kuma jarin da ta zuba ya kai kusan dala biliyan 7.

Ya jaddada cikakken tsarin kasarsa na bunkasa dangantakar tattalin arziki da ci gaba, da ɓangaren kiwon lafiya da samar da abinci da kula da muhalli.

Har ila yau, ya jaddada cewa akwai ofisoshin jakadancin Turkiyya 44 a faɗin Afirka da kuma ofisoshin jakadancin ƙasashen Afirka 38 a babban birnin Turkiyya.

A karshe Fidan ya yi kira da a yi wa Majalisar Dinkin Duniya garambawul, musamman samar da daidaito ta ɓangaren wakilci a Kwamitin Tsaro.

Ya kuma yaba wa kasashen Afirka bisa goyon bayan da suke bai wa al'ummar Falasɗinu, sannan ya jaddada muhimmancin muryar Afirka a ƙungiyoyin duniya kamar G20.

TRT Afrika