Daga cikin horon da suka samu har da na naƙaltar yadda za su kare manyan baƙi. / Hoto: AA Archive

Turkiyya ta horar da sojojin ƙasar Gambia, wadda ke shirin karɓar baƙuncin taron Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi OIC wanda za a gudanar a farkon watan Mayu.

Jumullar sojojin Gambia 351 ne suka samu horon na musamman ta ɓangarori da dama a Banjul babban birnin ƙasar, daga 7 zuwa 28 ga watan Afrilu.

Daga cikin horon da suka samu har da na naƙaltar yadda za su kare manyan baƙi.

Jakadan Turkiyya a Gambia Fahri Turker Oba da Ministan Harkokin Tsaro na Gambia Sering Modou Njie da Shugaban Sojojin Gambia Mamat Cham da sojoji da dama sun samu halartar wannan taro.

A lokacin taron, Oba ya bayyana cewa horon zai amfanar da sojojin na Gambiya kafin da kuma bayan taron.

Nijei a ɗayan ɓangaren, ya gode wa Turkiyya kan irin goyon bayan da take bayarwa domin ci gaban Gambia.

TRT Afrika