Mahukuntan Turkiyya sun bayyana cewa sun sanar da hukumar leken asirin Isra'ila game da duk wani yunkuri na aikata kisan gilla kan mambobin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da ke zaune a Turkiyya - kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito - hakan zai zo da sakamako mara daɗi.
Gargadin na jami'an gwamnatin Turkiyya da suka fitar da gargadin sun nemi a ɓoye sunayensu saboda rashin samun izinin magana da 'yan jaridu, ya biyo bayan labarin da mujallar Wall Street Journal ta fitar na zargin cewa a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare Gaza, tana kuma shirin kashe shugabannin Hamas da ke zaune a kasashen Turkiyya, Labanan da Qatar.
Ronen Bar, shugaban hukumar leken asirin cikin gida ta Isra'ila Shin-Bet (Shabak) a wani saƙon murya da aka fitar a tashar talabijin ta Istaila KAN ya ce Isra'ila 'ta kuɗuri aniyar kashe shugabannin Hamas a dukkan kasashen duniya da suka hada da Qatar da Turkiyya da Labanon, ko da a tsawon shekaru ne."
Jami'an na Turkiyya sun bayyana cewa an yi gargadin da ya kamata ga mahukuntan Isra'ila da lamarin ya shafa.
Da suke zantawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, jami'an na gwamnatin Turkiyya sun ambaci cewa a baya ma hukumomin leken asiri na kasashen waje sun yi yunkurin aikata aika-aika a Turkiyya amma ba sa yin nasara.
Sun jaddada cewa babu wata hukumar leken asiri ta kasar waje da za a bai wa damar yin wannan ta'annati a cikin kasar Turkiyya.
Mahukuntan Turkiyya sun la'anci hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza, waɗanda suka kashe kusan rayuka 16,000, suna kuma bayyana cewa kungiyar Hamas da Isra'ila ke son kakkaɓewa ba ƙungiyar ta'addanci ba ce.