Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana cewa akwai bukatar kungiyar Tarayyar Turai EU ta dauki matakai wadanda suka dace tare da yin adalci kan Turkiyya, kamar yadda majiyar diflomasiyyar Turkiyya ta bayyana.
Fidan da kwamishinan fadada harkokin kasashe masu makwabtaka na EU Oliver Varhelyi, sun gudanar da wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Lahadi, kan matsayar da majalisar kula da harkokin kungiyar ta EU ta cimma a ranar 12 ga watan Disamba da kuma sakamakon taron kolin kungiyar da aka gudanar a Brussels a tsakanin ranakun 14 da15 na watan Disamba, a cewar majiyar a ranar Litinin.
Fidan ya ce, bai dace a dage zaman tattaunawar hadin gwiwa da hukumar Tarayyar Turai da babban jami'in tsare-tsaren kungiyar EU Josep Borrell suka shirya kan alakar Turkiyya da Tarayyar Turai zuwa babban taron Kungiyar EU na gaba ba, duk da cewa an shirya zaman a taron da aka gudanar a makon jiya.
Ministan ya ce akwai bukatar kungiyar EU ta yi aiki ta hanyar dabaru tare da inganta dangantakarta da Turkiyya zuwa gaba, musamman a wannan zamani da duniya ke fama da tarin kalubale.
Fidan ya tunatar da cewa, Turkiyya na fatan kungiyar EU ta dauki kwararan matakai kan batutuwan da suka hada da sabunta kungiyar kasuwanci da kara hadin gwiwa kan zuba jari da kuma saukaka hanyoyin samun biza, in ji majiyar.