Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta aike sammaci ga babban jami'in da ke kula da ofishin jakadancin Denmark a Ankara, sakamakon ci gaba da muzanta Alkur'ani Mai Tsarki, kamar yadda majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya suka sanar da hakan.
Majiyar, wacce ta nemi a boye sunanta a ranar Talatar nan ta bayyana cewa "An aika sammaci ga babban jami'in da ke kula da ofishin jakadancin Denmark a Ankara, sakamakon maimaita wannan mummunan abu."
Majiyar ta kuma kara da cewa Turkiyya tana la'anta tare da nuna adawa ga wadannan aika-aika, kuma tana sake kira ga mahukuntan Denmark da su dauki matakan hana sake afkuwar hakan a nan gaba.
Matakin na zuwa ne bayan da aka kona Alkur'ani Mai Tsarki a gaban ginin ofishin jakadancin Turkiyya da ke Copenhagen a karo na biyu a jere.
A ranar Litinin ma Turkiyya ta gayyaci jakadun Denmark da Holan saboda ci gaba da wulakanta Alkur'ani Mai Tsarki a kasashensu.
A 'yan watannin nan masu nuna kyama ga Musulunci a Arewacin Turai na yawan kona Alkur'ani Mai Tsarki da cin zarafin Musulmai, wanda hakan ke janyo mayar da martani daga kasashen Musulmai da duniya baki daya.
Turkiyya ta sha nanata kiran a dauki matakan hana kai wa Musulunci hari karkashin '''yancin bayyana ra'ayi", tana kuma kira ga wadannan kasashe da ke bayar da kofar aikata aika-aikar da su gyara halayyarsu ta nuna kyama ga Musulunci.
Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmai (OIC) ma ta bayyana rashin jin dadinta ga wannan aika-aika, inda ta bayyana damuwa kan yadda wasu kasashe ke ci gaba da bayar da dama ga bata-gari suna yin wannan abu na aibu, sannan kuma ta ce yadda suke kasa daukar matakin hana hakan abin takaici ne.
Tarayyar Turai ma ta soki wannan mummunar dabi'a ta muzanta Alkur'ani Mai Tsarki.
A karshen watan Yuli Jami'in Harkokin Kasashen Waje na Tarayyar Turai Josep Borrel ya fitar da wata sanarwa inda ya ce "Tarayyar Turai na sake bayyana kudirinta da babbar murya wajen adawa da duk wani nau'i na nuna ingizawa da kyamatar wani addini."
A watan da ya gabata Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudiri da ke la'antar duk wani yunkuri na muzanta litattafai masu tsarki.
Majalisar ta "nuna rashin amincewa da duk wani yunkuri na kyamatar wani ko wasu saboda addinin da suke bi, ko kuma duk wani aiki da zai hari addini ko kayansu da suke girnama wa a addinance da litattafai masu tsarki da gidaje da kasuwanci da kadarori da makarantu da cibiyoyin raya al'adu da wuraren bauta, da ma dukkan wani nau'i na hari kan wuraren addini ko gine-gine ko dakuna."