Masana'antar Kayan Tsaro ta Turkiyya na ci gaba da bunkasa/ Hoto: TRT World

A shekaru 20 da suka gabata, Turkiyya ta yi babban kokari a fannin masana’antar kayan tsaro, wanda hakan ya rage dogaro da take yi kan kasashen waje da kaso 80 zuwa kaso 20, in ji Shugaba Erdogan.

A lokacin da yake bayani a ranar Lahadin nan a wajen bikin kaddamar da tankar yaki mai suna Altay da aka samar ga dakarun tsaron Turkiyya, Erdogan ya bayyana manufar Turkiyya ita ce “Ta zama mai cin gashin kanta a fannin tsaro”.

Ya ce “Mun rage dogaro ga kasashen waje don samun kayan tsaro daga kaso 80 zuwa kaso 20 a cikin kankanin lokaci na shekara 20. A shekarar 2002 ayyukan kayan tsaro ba su wuce 62 ba a Turkiyya, amma a yau akwai sama da 750.”

Shugaban na Turkiyya ya kuma kara da cewa a lokacin da kasafin kudin Turkiyya ke ware dala biliyan 5.5 a 2002, a yau adadin ya kai dala biliyan 75.

Erdogan ya kuma ce kowanne aiki na fannin tsaro da ake yi na bukatar lokaci na tsawon shekaru da hakuri da aiki tukuru da kuma kudade.

Ya kuma kara da cewar Turkiyya ta zama mai fitar da kayayyakin tsaro zuwa kasashen ketare inda dakarun soji da dama ke amfani da kayayyakinta.

TRT World