Turkiyya na ɗaukar matakan hanzarta shirinta na sayen jiragen sama na yaƙi samfurin 'Eurofighter Typhoon', kamar yadda wani jami'in ma'aikatar tsaro ya tabbatar.
A baya birnin Ankara ya bayyana tattaunawar da yake yi da ƙasashen da ke ƙera Eurofighter da suka haɗa da Birtaniya da Sifaniya, don ganin ya mallaki jiragen na Typhoon, duk da nuna ƙin amincewa da Jamus ta yi. Sai dai kuma, tuntuni Turkiyya ta bayyana damuwarta kan rashin cigaba, tana nuna halin ko-in-kula daga Jamus ne musabbabin jan-ƙafar.
A watan jiya, Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya gana da Firaministan Jamus Ola Scholz a wani ɓangare na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya, inda aka tattauna kan batun.
Shugabannin biyu sun shirya za su sake ganawa a Istanbul a rana 19 ga Oktoba, inda batun sayen jiragen yaƙi samfurin Eurofighter zai kasance a kan gaba tsakani batutuwan da za a tattauna.
Da aka tambaye shi game da sha'awar mallakar jiragen yaƙi na Eurofighter da Turkiyya ta nuna sha'awar mallaka, Scholz a ranar Alhamis ya tabbatar da suna cikin batutuwan da za a tattauna.
"Tabbas, a koyaushe muna tattauna kai makamai ga ƙawayenmu a NATO," in ji shi, yana mai cewa a yanzu Birtaniya na tattaunawa da gwamnatin Turkiyya.
"Babu wasu sharuɗɗa da aka gindaya"
"Ana ayyukan ganin an sayi jiragen na Eurofighter. Ayyukan na da manufar hanzarta sayen jiragen. Babu wasu sharuɗɗa da aka gindaya," in ji jami'in ma'aikatar tsaron ta Turkiyya.
Ƙasashen Jamus, Birtaniya, Italiya da Sifaniya tare da saka hannun kamfanoni irin su Airbus, BAR Systems da Leonardo ne ke ƙera jiragen yaƙi samfurin Eurofighter Tayphoon.
Baya ga shirin sayen waɗannan jiragen, Turkiyya, wadda mamba ce ta NATO, a baya-bayan nan ta ƙulla yarjejeniyar sayen jiragen yaƙi samfurin F-16 guda 40 da ƙunshi 79 na kayan sabunta jiragen da take da su da Amurka.
Ankara ma na ƙera nata jirgin sama na yaƙi mai suna KAAN.