Ƙasar Turkiyya na fatan bunƙasa harkokin kasuwancinta da ƙasar Saudiyya zuwa $30b a matsakaicin zango, kamar yadda mataimakin shugaban ƙasar Turkiyya Cevdet Yilmaz ya faɗa a wajen wata walimar cin abincin dare da aka shirya ta taron zuba jari tsakanin Tukiyya da Saudiyya da aka yi a birnin Istanbul.
A wajen walimar da aka gudanar ranar Alhamis, Yilamz ya ce cinikayyar da aka yi tsakanin ƙasasahen biyu ta kai ta $6.8B a 2023, yayin da kamfanonin Saudiyya suka zuba jari da ya kai na dala biliyan biyu a Turkiyya kawo yanzu.
"Muna ganin za mu iya burin bunƙasa yawan cinikayyar da muke yi ta yadda kowane ɓangare zai amfana kuma cikin sauri zuwa dala biliyan 10 cikin gajeren zango, a cewarsa.
Yilmaz ya ce Turkiyya na sawun gaba a matsayin nahiya, wajen fitar da kaya da zuwa jari tun bayan annobar korona.
"Turkiyya na ba da dama ga masu zuba jari a fannin kimiyya, da tsaro, da samar da makamashi da ba ya gurɓata mahalli, da harkokoin albarkatun man fetur, da harkar kuɗaɗe, da yawon buɗe ido, da kuma gine-gine a matsayin wani ɓangare na zuba jari na ƙasa da ƙasa," kamar yadda ya fada.
"Ɓangarorin Saudiyya da suka yi wa masu jari bayani sun haɗa da sinadarai, masu ƙere-ƙeren injina, da masana'antun sarrafa abinci da kayan shaye-shaye, da sababbin fasahohi, da harkokin abubuwan hawa, da ɓangaren jiragen sama da magunguna, da kayan kula da lafiya, da harkokin soja, da makamashin da ba ya gurɓata mahalli, da kayan gine-gine, da kuma harkar haƙar ma'anadanai," a cewarsa.
Dangane da ganawarsa ministan yawon buɗe ido na Saudiyya Ahmed AlKhateeb kuwa, Yilmaz ya ce "mun nuna gamsuwa da yadda adadin masu zuwa Turkiyya yawon buɗe ido daga Saudiyya ya ƙaru zuwa kaso 70 a 2023, inda ya kai kimanin 830,000, mun kuma yi duba kan adadin ƴan ƙasarmu dake ziyarar Saudiyya daga Turkiyya da ya ƙaru fiye da sau uku da rabi, inda ya kai mutum 670,000 a 2023.
"Mun kuma amince gaɓa ɗaya cewa ya kamata a sake duba damammakin da ake da su a fannin yawon bude ido tsakanin Saudiyya da Turkiyya," kamar yadda ya bayyana.
Yilmaz ya ƙara da cewa, gudunmuwar da alaƙar ƙut-da-ƙut kuma tattaunawa mai ƙarfi ta siyasa tsakanin shugabannin ƙasashen biyu za su bayar a fannin haɗakarmu ta tattalin arziki, za su ƙara inganta haɗakarmu."
"Yayin da Turkiyya za ta ci gaba da bai wa masu zuba jari ƴan Saudiyya muhimman damammaki, Saudiyya ita ma ta ci gaba da samar da muhimman yanayi mai kyau ga masu zuba jarinmu na Turkiyya," a cewarsa.