Ma’aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta bayyana cewa Majalisar Dattawan Faransa ta zubar da mutuncinta bayan karbar bakuncin ‘yan ta’addar PKK/YPG tare da ba su lambar girma.
Ma’aikatar ta kara da cewa “Marabtar ‘yan ta’adda masu zubar da jini a Majalisar Dokokin Faransa mambar kawancen NATO ya zubar da mutuncin kasar.”
Wannan sanarwa ta fito kwana guda bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta aika sammace ga Jakadan Faransa Herve Magro don la’antar wannan aika-aika.
Majiyoyin diplomasiyya na Turkiyya sun rawaito cewar an bayyanawa Magro irin barazanar ta'addancin da ‘yan ta’addar a ware na PKK/YPG/PYD da SDG suke yi a Turkiyya da SIriya.
Ma’aikatar ta kara da cewa “Wannan mataki ya sabawa ruhin kawance kuma cin dunduniyar ayyukan yaki da ta’addanci da NATO ke yi ne”.
Gwamnatin Ankara na sauraron mahukuntan Faransa ba za su goyi bayan ayyukan da za su halasta kungiyar ta’adda ta kasa da kasa da kuma yaduwar ta a Siriya ba.
Tsawon shekaru sama da 35 da suka gabata, PKK da kasashen Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka aiyana a matsayin kungiyar ta’adda na aikata ta’addanci a Turkiyya inda ta kashe sama da mutane dubu arba’in da suka hada da mata da yara kanana.