Erdogan ya sha alwashin sake gina lardi 11 da girgizar kasa ta lalata ranar 6 ga watan Fabrairu / Photo: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da manufofin jam’iyyarsa ta Justice and Development (AK) gabanin zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki da za a yi ranar 14 ga watan Mayu.

Erdogan ya bayyana manufofin ne ranar Talata a Ankara, babban birnin kasar.

Ya kara da cewa abu na farko da zai mayar da hankali a kai shi ne sake gina wurare da inganta rayuwar mutanen da girgizar kasar 6 ga watan Fabrairu ta shafa a yammacin kasar.

"Duk wani hari, duk wani bala’i da muka fuskanta, musamman girgizar kasar 6 ga watan Fabrairu na nuna bukatar mu zage dantse wajen kara hada kawunanmu da kyautata ‘yan uwantakarmu," in ji Erdogan.

Ya kara da cewa: "Za mu warke baki daya daga ciwon da muka ji sakamakon girgizar kasar da ta auku a ladi 11 ta hanyar gina sabbin gidaje 650,000, daga cikinsu za a kammala 319,000 a shekara daya."

Shugaba Erdogan ya ce an samar da shirin "kasa baki daya na tsarin kare bala’i," yana mai cewa hakan zai sa larduna 81 su jure wa aukuwar girgizar kasa.

Ya sha alwashin habaka tattalin arziki Turkiyya nan gaba, inda Erdogan ya ce: "Turkiyya ba ta da wani zabi da ya wuce ta jajirce da kuma kara karfinta domin kada ta fada kangin siyasa da tattalin arziki."

Da yake tsokaci kan tattalin arziki, Erdogan ya ce Turkiyya na shirin rage hauhawar farashi matuka, inda ya kara da cewa: "Za mu kara walwala ga ma’aikatanmu, daga ma’aikatan gwamnati zuwa ‘yan fansho, ta hanyar kara musu kudi domin rage radadin hauhawar farashi."

Ya ce Turkiyya za ta ci gaba da zuba jari da samar da kayayyaki da fitar da su kasashen waje har sai ta cimma manufarta ta inganta kasuwancin da kasashen waje zuwa $1 tr.

'Tsarin Turkiyya'

Turkiyya za ta ci gaba da zama bisa hanyar zaman lafiya a "matsayinta na kasar zaman lafiya da tsaro" a yayin da duniya ke fuskantar karin kalubale, a cewar Erdogan.

Ya ce: "Za mu gina tsarin Turkiyya inda manufofinmu na kasashen za su tabbatar da zaman lafiya da kyautatuwar dangantaka da hadin kai da diflomasiyya a gare mu da dukkan dan adam".

Ya tuna wa mahalarta taron cewa Turkiyya tana ita yin sulhu da dukkan bangarorin da ke yakin Rasha da Ukraine, sannan ta kawo cigaba a yarjejeniyar fitar da hatsi tsakaninsu da yin musayar fursunoni da kuma yiwuwar tabbatar da zaman lafiya.

Kazalika ya ce Ankara tana yaukaka dangantaka da kasashen Musulmai ba tare da ta nemi izini daga wurin kowa ba.

Da yake bayani kan cigaban da aka samu ta fannin tsaro, Erdogan ya ce Turkiyya ta yi nasarar bunkasa shi "a kankanen lokaci inda kasashen duniya ke kishinta."

"Mun samar da kayayyakin tsaro fiye da bukatunmu, don haka muna samun cigaba don zama babbar kasa a fannin tsaro wadda za ta iya fitar da makamai zuwa kasashe 170, ciki har da fitar da kayan yaki irin su UAVs, UCAVs, makamin Akincis [samfurin Baykar mai cin dogon zango ], motoci da jiragen ruwa na tsaro," in ji shi.

Shugaban Turkiyya ya ce kasar za ta kara karfi a fannin makamashi da harkokin noma da ilimi da sufuri.

AA