Türkiye ta kama ‘yan ta’addan PYD/PKK da ke kokarin shiga kasar daga Siriya

Türkiye ta kama ‘yan ta’addan PYD/PKK da ke kokarin shiga kasar daga Siriya

Türkiye na ayyukan yaki da ta'addanci a ciki da wajen kasar.
    Türkiye da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana PKK a matsayin kungiyar ta'adda/ Photo TRT World

Jami’an tsaron Türkiye sun kama ‘yan ta’addar a ware na PYD/PKK biyu a lokacin da suke kokarin shiga kasar ta barauniyar hanya a kan iyakar kudu maso-gabas da ke lardin Sanliurfa.

Majiyar da ta nemi a boye sunanta saboda rashin samun izinin magana da kafafen yada labarai, ta bayyana cewa jami’an tsaron sun bi sahun ‘yan ta’taddar kan iyakar Sanliurfa da aka tsaurara matakan tsaro, a lokacin da suke yunkurin shiga Türkiye.

Majiyar ta kara da cewa an kai ‘yan ta’addar asibiti don bincikar lafiyarsu, sannan ana kuma ci gaba da yi musu tambayoyi.

Ba a bayyana sunayen ‘yan ta’addar ba.

Wannan kame wani bangare ne na ayyukan tabbatar da tsaro da jami’an Türkiye ke yi.

A farkon wannan watan an ruwaito jami’an Sojin Türkiye sun kashe wani babban dan ta’addar PKK da Turkiye ke nema ruwa a jallo, tare da karin wasu ‘yan ta’adda shida a yankin kudu maso-gabashin kasar.

A hare-haren da kungiyar ta’adda ta PKK ta kai a fiye da tsawom shekara 35, ta kashe mutum sama da 40,000 da suka hada da mata da yara kanana.

Kasashen Türkiye da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana kungiyar PKK a matsayin ta ta’addanci.

Kungiyar PYD ce reshen PKK a kasar Siriya.

TRT World