Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce sun yi bakin ciki da samun asarar rayuka sakamakon zaftarewra kasa a Ethiopia. Photo: AA

Turkiyya ta miƙa ta'aziyya ga Ethiopia bayan zaftarewar kasar da mamakon ruwan saman da aka samu ya janyo.

A wata sanarwa da ta fitar, Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce ta yi "baƙin ciki" da samun rasa rayuka bayan zaftarewar kasar da afku. "Muna miƙa sakon ta'aziyya da jaje ga jama'ar Ethiopia," in ji sanarwar.

Zaftarewar kasa ta afku a kudancin Gofa a ranar Litinin, inda mutum sama da 200 suka mutu, kamar yadda gwamnatin yankin ta sanar.

Ana yawan samun zaftarewar kasa a kudancin Ethiopia a lokacin damina a tsakanin watannin Yuni da Agusta. Amma wannan ne mafi muni da janyo asarar rayuka.

"Ya zuwa yanzu, mutane 229 ne suka mutu, maza 181 da mata 81, Ana ci gaba da bincke don kubutar da mutane," in ji sanarwar da wakilin Yankin Kudancin Kasar ya fitar ranar Talata.

Ceto da hannu

Adadin wadanda za su mutu na iya ƙaruwa saboda yadda yankin da ibtila'in ya samu yake a waje mai nisa da za a iya wahalar kai manyan injinan ceto kamar yadda mahukunta suka bayyana.

An fara aikin ceton da haƙa da hannu, in ji wani jami'in yankin da ya nemi a ɓoye sunansa.

Wani jami'in yankin, Misikir Mitiku, ya shaida wa manema labarai cewa masu ceto na daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, inda wasunsu suka bata a yayin da suke neman wasu.

Bayan afkuwar mummunar zaftarewar ƙasar, Gwamnan Dagmawi Ayele ya fitar da sanarwar bayyana bukatar samar wa da jama'a kayayyakin tunkarar irin wannan ibtila'i a nan gaba.

"Ibtila'in ya afku kafin 12 na rana, a lokacinda mutane suka taru don ganin irin yadda ruwa ya zuba sosai a daren Lhadi, kuma zaftarewar ta danne mutanen da suka rufta," in ji wani jami'i daga ofishin yada labaran yankin.

Masu aikin ceto da suka hada da jami'an yankin da malaman makaranta da 'yan sanda na daga cikin wadanda suka mutu, in ji shi.

Ya kara da cewa har yanzu ba a gama gano cikakkiyar illar da zaftarewar kasar ta janyo ba.

TRT Afrika