Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki tsarin kasashen duniya da cewa an tsara shi ne don wasu zababbun ƙasashe 'yan gata su ci gajiyarsa, inda ya buga misali da abubuwan da ke faruwa a Gaza.
"Abin da ke faruwa a Gaza hujja ce ƙwaƙƙwara ta cewa an tsara tsarin kasa da kasa ta yadda ake amfani da shi wajen cin zarafin wasu 'yan tsiraru," in ji Fidan a ranar Talata yayin taron diflomasiyya kan makomar Falasdinu a Ankara.
Ya kuma bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin kisan ƙare dangi, yana mai cewa an kashe mutum 42,000 galibi mata da ƙananan yara, da ganganci da kuma tsari.
Bugu da ƙari, Fidan ya jaddada cewa wannan bala'in ba sabon abu ba ne, amma an shafe shekaru 70 ana yi, ya kuma nuna matukar ɓacin rai kan halin ko oho na ƙasashen duniya.
"Abin takaici, kasashen duniya da suka fara da kanmu, da al'ummar Musulmi, da kuma al'ummar Larabawa, ba su da wani amfani, ba su da karfi, da rashin fata wajen daƙile wannan bala'i da ke faruwa."
Ya soki yunƙurin kare kisan da ake yi tare da yin tir da yadda ake amfani da ƙirƙirarriyar basira (AI) a cikin ayyukan soji, suna cewa, "Ba mu ba ne. Wannan na'ura ce, tana kisa."
Ministan Harkokin Wajen na Turkiyya ya kuma nanata matsayin Turkiyya kan samar da kasashe biyu a matsayin hanya daya tilo da za ta samar da zaman lafiya, yana mai cewa, "Idan Falasdinawa na da kasarsu, da kasa, da 'yanci, da mutuncinsu, me ya sa za su bukaci yin yaki?"
Ya kuma yi kira ga al'ummar duniya da su matsa ƙaimi wajen ganin an samar da kasashe biyu, yana mai cewa sama da kasashe 150 ne suka amince da Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya.
Ya kuma yi kira ga al'ummar duniya da su matsa ƙaimi wajen ganin an samar da kasashe biyu, yana mai cewa sama da kasashe 150 ne suka amince da Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya.
Fidan ya bukaci daukar matakin gaggawa, inda ya yi gargadin cewa, matukar ba a samar da mafita ba, rikicin zai rikide zuwa wani babban rikicin yanki da na duniya baki daya.
"Isra'ila ta yi rashin nasara a yakin"
Ministan Harkokin Wajen kasar Jordan kuma ya ce samar da kasar Falasdinu shi ne jigon zaman lafiya a yankin.
Ayman al Safadi ya shaida wa taron cewa, in ba a kafa kasa mai cin gashin kai ga Falasdinawa ba, Isra'ila ba za ta samu zaman lafiya ba.
Ya ce ba abin da Isra’ila ke yi sai ɓarna da jawo halaka kawai a yankin.
Ya ƙara da cewa, "Isra'ila ba ta neman zaman lafiya da kwanciyar hankali ga kasashen yankin, kamar yadda ta lalata Gaza da kuma fadada hare-harenta a kan Lebanon."
“Isra’ila ta yi rashin nasara a yaƙin ta fuskar siyasa da kuma ɗabi’u,” in ji Safadi.
Babban jami'in diflomasiyyar ya jaddada cewa, babu wata motar daukar kaya guda daya da aka bari zuwa cikin Gaza tun ranar 30 ga watan Satumba a ci gaba da yakin da take yi a yankin.
"Isra'ila na ci gaba da jefa bama-bamai a matsugunai da asibitoci, da makarantu," in ji shi. "Isra'ila tana fadada ikonta a kan wasu yankunan Falasdinawa da ta mamaye ta hanyar gina ƙarin matsugunai ga al'ummarta."
"Abin da Isra'ila ke yi laifi ne na yaƙi," in ji Safadi.