Tauraron dan Adam din wanda shi ne irinsa karo na biyar da kasar ta yi zai wuce shekara 35 yana aiki saboda sabuwar fasahar da aka yi shi da ita. Hoto: AA Archive

Tauraron dan Adam din da kasar Turkiyya ta samar mai suna Turksat 5A yana ci gaba da kara fito da sunan kasar a fannin sadarwa inda yake amfani da tsarin Ku band, wanda hakan ya sanya Turkiyya a sahun kasashe kalilan da suke aiki da fasahar zamani inganci mai suna High-frequency electromagnetic spectrum.

Ministan Sadarwa da Abubuwan More Rayuwa Abdulkadir Uraloglu ya ce Turksat 5A ya fara aiki a falaki tun shekarar 2021, inda ake amfani da tsarin Ku band wanda yake bayar da damar sadarwa mai inganci.

“Ana amfani da na’urori na zamani wanda zai iya samar da hotuna masu inganci sosai da ya kai 8K yayin yada shirye-shirye a talabijin daga tauraron dan Adam na Turksat 5A, an samu ci gaba sosai kan ingancin hotuna talabijin wanda hakan ba karamin nasara ba ce,” in ji Uraloglu.

Ministan ya ce tauraron dan Adam din ya bayar da damar yada shirye-shirye da sadarwa a fadin nahiyar Turai da yankin Gabas ta Tsakiya da Afrika da kuma tekuna uku da ke kewaye da Turkiyya.

“Turksat 5A ya samar da hanyar warware matsaloli a duniya kuma ana amfani da wajen aiki a karkashin teku inda ake bayar da sakamako mai inganci,” in ji shi.

Zai kwashe lokaci mai tsawo ana cin amfaninsa

“An fara samun kudin shiga sosai daga kasashen ketare musamman daga kamfanin Saudiyya mai suna Arabsat, wanda yake amfani da tauraron dan Adam na Turksat 5A,” in ji Uraloglu.

Sannan ministan ya ce tauraron dan Adam, wanda shi ne karo na biyar da kasar ta yi, za a ci moriyarsa har fiye da shekara 35 saboda sabuwar fasahar da aka yi shi da ita mai suna Electric propulsion system.

“Turksat 5A ya samu wuri a falaki wato 31 degrees East orbit har zuwa shekarar 2056,” in ji shi.

“Sabuwar fasahar Electric propulsion system da yake amfani da ita ta sa ba ya bukatar makamashi sosai kafin ya fara aiki kuma hakan ya rage masa nauyi,” in ji Ministan.

TRT World