Murat Kurum shugaba ne kwararre kuma mai hangen nesa. An zabe shi a matsayin dan takarar Magajin Birnin Istanbul karkashin Jam'iyyar AK, kuma a matsayinsa na matashi, kwararre ne wanda ke da tarihin kyawawan ayyuka a gwamnati.
Abokin hamayyarsa shi ne magajin birnin Istanbul na yanzu da ke takara karkashin CHP Ekrem Imamoglu da ya hau kan mulki tun 2019. Kasancewarsa zababben dan majalisar wakilai karkashin AKP a watan Mayun bara, a yanzu Kurum ne shugaban Kwamitin Kula da Muhalli na Majalisa.
An haifi Kurum a Ankara a shekarar 1976, kuma ya fara ayyukansa na gwamnati cikin nasara tare da inganta rayuwar jama'a, ya zama abin misali na matashi kuma kwararre a zamanance.
Bayan ba shi takara, Kurum ya bayyana jerin manufofinsa da yake son cim ma ta hanyar bin sahun tsohon magajin garin Istanbul kuma shugaban kasa a yanzu Recep Tayyip Erdogan.
Kurum ya sha nanata irin darussan da ya koya daga mai gidansu Erdogan, wanda ya sauya Istanbul zuwa babban birni bayan ya zama magajin birnin a 1994.
Kurum ya bayyana shirinsa na dorawa daga inda Shugaba Erdogan ya tsaya wajen inganta rayuwar jama'ar Istanbul da samar da ayyukan ci-gaba gare su.
Matashi Mai Karsashi
A shekaru 47, Kurum ya yi kokari sosai wajen warware matsaloli da dama. Kwarewarsa ta sanya ba shi da tsara, inda ya san matsalolin dimbin matasa da sauran jama'ar Istanbul.
Kokarinsa wajen kulla mu'amala da matasa shaida ce da ke nuna kaunarsa ga ci-gaban birnin, wanda ke bayar da haske ga warware matsaloli da kalubalen birnin a zamanance.
Nasara a matsayin Minista
A lokacin da yake da shekara 42, tafiyar siyasar Murat Kurum ta kai babban matsayi inda ya fara aiki a matsayin Ministan Kare Muhalli da Tsara Birane na Turkiyya a shekarar 2018. A tsawon lokacinsa na Minista, ya gudanar da shugabanci mai kyau, ya jagoranci gudanar da manyan ayyuka na ci-gaban kasa.
A karkashin kulawarsa, a 2021 ma'aikatar ta kaddamar da manyan ayyuka da sauye-sauye, da taken "Ma'aikatar Muhalli, Tsara Birane da Yaki da Sauyin Yanayi". Kokarin Kurum wajen kyautata muhalli da kare yanayi, na bayyana manufarsa wajen gina Istanbul ya zama birnin mai kyawun.
Sadaukarwa lokacin girgizar kasa
Daya daga cikin lokutan da aka ga kwarewar Murat Kurum shi ne lokacin da girgizar kasa ta afku a ranar 6 ga Fabrairu. Ya kasance a yankin da ibtila'in ya afku, ya duba yankin sosai ina ya ziyarci wurare kusan miliyan shida a larduna 11.
Ya mayar da hankalinsa kacokan ga yunkurin daukar matakan da suka dace bayan afkuwar girgizar kasar inda ya samu goyon bayan jama'a. Wannan lokaci mai muhimmanci ya sake tabbatar da shi a matsayin jagora da ba iya ayyukan gaggawa da jinkai ya fahimta ba, har ma da shiryawa don daukar matakan da suka kamata a lokacin da ya dace.
Sadaukarwar da Kurum ya yi wajen aiki da kwarewa don sake gina yankunan da girgizar kasa ta illata na nuni da kwarewarsa wajen son inganta rayuwar jama'ar Istanbul.
Kwarewar da Kurum ya samu yayin aiki da Hukumar Samar da Gidaje ta Turkiyya (TOKI), na kara fayyace iyawa da kwarewarsa wajen yaki da matsalolin gurbata muhalli, wadanda za su iya illata wasu gundumomin Istanbul.
Buri a matsayin magajin gari
A matsayin dan takarar magajin garin Istanbul, Murat Kurum ya tattaro manufofin da za su ciyar da birnin Istanbul gaba. Ya mayar da hankali kan kaddamar da manyan ayyukan magance samuwar wata illa idan aka samu girgizar kasa, yana mai nufin samar da birnin mai karfin gine-gine.
Kurum na son samar da Istanbul da ke dauke da zamananci, a yayin da ake kuma kare martabar tarihi da al'adun birnin - birnin da zai mayar da hankali wajen kirkirar sabbin kayan cigaba masu dorewa d akuma tafiya tare da kowanne bangare.
Tare da digiri na biyu a fannin Sauya Birane, Kurum na da karsashin samar da karin manyan kayan more rayuwa a Istanbul da kuma magance matsalar cunkoson ababan hawa da ke addabar birnin.
A takaice dai, takarar Kurum na gabatar da matashi, kwararre kuma mai karasashin hidimtawa mutane. Nasarar da ya yi a matsayin Minista, gami da sadaukarwar da ya yi bayan afkuwar girgizar kasa, lokacin da ake fuskantar kalubale, na bayyana shi a matsayin shugaban da zai iya jagorantar istanbul tare da kai birnin da jama'arsa tudun mun tsira.