Turkiyya ta karbi bakuncin zagayen farko na tattaunawar zaman lafiya tsakanin Somalia da Ethiopia, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta sanar.
Tattaunawar wadda ke nuna wani muhimmin mataki na aiwatar da Yarjejeniyar Ankara da aka amince da ita a ranar 11 ga watan Disamba, 2024, wadda aka gudanar a birnin Ankara a ranar Talatar, karkashin jagorancin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, ta tattaro tawagogi karkashin jagorancin Ministan Harkokin Wajen Habasha Gedion Timothewos da Ministan Harkokin Wajen Somaliya Ali Mohamed Omar.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne ya jagoranci Yarjejeniyar ta Ankara, bayan tattaunawa tsakanin Firaministan Habasha Abiy Ahmed da Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud.
Yarjejeniyar ta fitar da wani shiri na samar da kwanciyar hankali da haɗin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.
A yayin tattaunawar, tawagogin biyu sun sake jaddada aniyarsu kan ka'idojin da aka tsara a cikin yarjejeniyar, tare da jaddada bukatar ƙara tattaunawa da hadin gwiwa mai ma'ana.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan mayar da wannan mafarkin zuwa matakai masu ma'ana da za su amfani kasashen biyu da kuma ba da gudunmawa ga ci gaban yankin na tsawon lokaci.
Haɗa kai domin ci gaba mai ɗorewa
Bayan kammala zagayen farko na tattaunawar, duka ɓangarorin biyu sun nuna aniyarsu ta dasa wani tubalin gina abin da zai amfane su baki ɗaya domin samun ci gaba mai ɗorewa, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana.
Haka kuma wannan tattaunawar na nuni da wani mafari na tunkarar maganace matsalolin tattalin arziki da ƙalybalen siyasa da kuma ƙara yauƙaƙa diflomasiyya tsakanin Sonmalia da Ethioia.
Turkiyya wadda ta dade tana fafutukar tabbatar da zaman lafiya a yankin Kusurwar Afirka, ta jaddada aniyar ta ta tallafa wa shirin samar da zaman lafiya.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta jaddada cewa, Ankara na ci gaba da jajircewa wajen tattaunawa da kuma shirya zagaye na gaba na tattaunawa ta gaba da ake sa ran gudanarwa a Maris ɗin 2025