Shugabannin kasashen duniya da dama sun taya Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya murna kan sakamakon zabukan kasar, kamar yadda Ma'aikatar Sadarwa ta Turkiyya ta ce.
Ma'aikatar Sadarwar a ranar Laraba ta ce daga cikin shugabannin da suka taya Erdogan murna akwai Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani da Shugaban Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, da Firaministan Hungary Viktor Orban da Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim da kuma Shugaban Gwamnatin Yanki na Kurdawa (KRG), Nechirvan Barzani.
Sun yi wa Erdogan fatan alheri da nasara a zagaye na biyu na zaben da za a yi.
Miliyoyin mutane ne suka kada kuri'unsu a ranar 14 ga watan Mayu don zabar shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki 600.
Kawancen Al'umma na Erdogan ne ya samu nasara mafi rinjaye a majalisar dokokin, yayin da za a fafata a zagaye na biyu na zaben ranar 28 ga watan Mayu, duk da cewa Erdogan ne a kan gaba a zagayen farko.
Erdogan da babban abokin karawarsa Kemal Kilicdaroglu, shugaban babbar jam'iyyar adawa ta (CHP) kuma dan takarar jam'iyyu shida na Kawancen 'Yan Kasa, za su fafata a zagaye na biyun.