Rahotanni sun bayyana cewa Fetullah Gulen wanda ya kitsa yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar Turkiyya a shekarar 2016 ya rasu a jihar Pennsylvania ta Amurka. Ya rasu yana da shekara 83.
Herkul, shafin yada farfaganda na kungiyar ta'addancin, ya bayyana a shafinsa na X cewa Gulen ya rasu a ranar Lahadi da yamma a asibitin da yake jinya.
Shekaru da dama, Gulen, shugaban kungiyar 'yan ta'adda ta Fetullah (FETO), yana kula da babbar ƙungiyar ta'addanci da ke da nufin zagon kasa ga Turkiyya da kuma dimokuraɗiyyar ƙasar.
Gulen ya kasance yana zaune a jihar Pennsylvania ta Amurka kafin rasuwarsa. Shugabannin Turkiyya dai sun dade suna neman a mika shi, amma jami'an shari'a na Amurka ba su amince da hakan ba.
Kungiyar ta'adda ta FETO da shugabanta Fethullah Gulen ne suka kitsa juyin mulkin da ba yi nasara ba a ranar 15 ga watan Yulin 2016 a Turkiyya inda aka kashe mutane 252 tare da jikkata wasu 2,734.
Har ila yau, Ankara na zargin kungiyar ta'addanci ta FETO da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin kasar ta hanyar kutsawa cibiyoyin kasar Turkiyya, musamman sojoji da 'yan sanda da kuma bangaren shari'a.