Ana saran tattaunawar za ta tabo batutuwan da suka shafi duniya musamman yakin Isra’ila da Hamas a Gaza da sauran yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Hoto: AA Archive

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai kai ziyara Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) daga ranakun 12 zuwa 13 ga Fabrairu, kuma zai kai ziyara Masar ranar 14 ga Fabrairu, kamar yadda ma’aikatar yada labaran kasar Turkiyya ta bayyana.

Erdogan zai halarci Babban Taron Gwamnatocin Kasashe wanda za a yi a Dubai a ranar Talata, 13 ga Fabrairu a matsayin bako na musamman, kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar ta bayyana a ranar Lahadi.

Shugaban Turkiyya zai yi jawabi a wajen taron a matsayin babban mai jawabi kuma ana sa ran zai tattauna da wasu takwarorinsa shugabannin kasashe da suka halarci taron musamman Shugaban UAE Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.

Babban taron zai samu halarcin manyan jami’an gwamnati daga kasashe daban-daban da shugabannin manyan kungiyoyi da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu da malaman jami’o’i da kungiyoyin fararen-hula da shugabannin manyan cibiyoyin nazari da ’yan jarida da kuma ’yan kasuwa.

Yayin ziyarar Erdogan a birnin Alkahira, ana sa ran za a dauki wasu matakai don bunkasa dangantaka tsakanin Turkiyya da Masar.

Tattaunawar za ta fi mayar da hankali ne kan batutuwan da duniya ke fuskanta kamar matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya musamman hare-haren da Isra’ila take kai wa Gaza da sauran yankunan da Falasdinawa da aka mamaye.

Shugaban Turkiyya Erdogan zai tattauna halin da ake ciki a Gaza da takwaransa na UAE.

Turkiyya ta mika sakon ta’aziyyarta

A ranar Lahadi Turkiyya ta mika sakon ta’aziyyarta ga UAE da Somaliya da kuma Bahrain dangane da mummunan harin ta’addanci da aka kai wani sansanin sojoji a Somaliya a Babban Birnin kasar Mogadishu.

“Muna bakin cikin arasar rayukan sojoji, wadanda suka taimaka wajen samar da tsaro a Somaliya, sanadin harin ta’addancin da ya faru ranar 10 ga watan Fabrairu a Mogadishu,” a cewar sanarwar Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.

Tun da farko Ministan Tsaron UAE ya ce an kashe sojojin kasar hudu da kuma wani sojan Bahrain “yayin da suke bakin aikinsu.”

Wani karamin soja ne ya bude huta kan masu bai wa sojojin UAE shawara a wani sansanin sojoji a birnin Mogadishu, kamar yadda mahukuntan Somaliya suka bayyana.

Kasar Somaliya ta kwashe tsawon lokaci tana fama da matsalar tsaro, inda kasar ta fi fuskantar barazana daga kungiyoyin Al Shabab da Daesh.

TRT World