Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Laraba ya gana da Shugaban Mulkin Sojin Sudan Abdel Fattah al Burhan a babban birnin Turkiyya, Ankara.
Sai dai ba a yi karin bayani ba dangane da ganawar sirrin da suka yi a fadar shugaban kasa.
Ziyarar ita ce ta biyar da al Burhan ya yi wanda shi ne shugaban sojin Sudan tun bayan yaki ya barke tsakanin sojojin Sudan da Rundunar RSF a watan Afrilu. Tun da farko ya kai ziyara Masar da Sudan ta Kudu da Qatar da kuma Eritriya.
Tun ranar 15 ga watan Afrilu, sojojin Sudan suka fara yaki da Rundunar RSF karkarshin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.
Bayan shafe watanni yana zaune a hedkwatar sojoji a birnin Khartoum, Burhan ya fara fita daga hedikwatar a watan jiya inda ya kai ziyara ga kawayen kasarsa a makonnin da suka wuce.
Ya kasance ne a birnin Port Sudan a gabashin kasar, wanda ba a fada a can – abin da ya sa jami'an gwamnati da ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya suka koma can.
Kuma nan ne kawai akwai filin jirgin saman da ke aiki.
Akalla fararen-hula 5,000 ne suka mutu sasakamakon yakin basasar, kamar yadda kungiyar Armed Conflict Location & Event Data Project ta bayyana.
Yakin ya yi sanadin raba mutum miliyan 4.8 daga muhallinsu – miliyan daya daga cikinsu sun ketara iyakar kasar – kuma Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa adadin zai karu.