Jirgin wanda aka fara kera shi a shekarar 2016, an kammala shi ne a watan Maris /Hoto: AA

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da cewa sunan sabon samfurin jirgin yakin da ya kaddamar TF-X, is KAAN.

“A yanzu Turkiyya ta bunkasa a kowane fanni – a kasa da ruwa da sama har ma da sararin samaniya,” a cewar Shugaba Erdogan a wajen wani biki da aka yi a ranar Litinin a Ankara.

Kamfanin Kera Jiragen Sama na Turkiyya TAI ne ya shirya bikin don gabatar da sabbin jiragenta ciki har da KAAN.

Kamfanin TAI ne ya kera jirgin yakin na KAAN da nufin maye gurbin jirgin sojin Turkiyya mai kirar F-16 da ya tsufa.

Kera wannan jirgin zai sa Turkiyya ta zama daya daga cikin kasashe biyar da suke da irin wannan fasahar a duniya, in ji Erdogan.

Jirgin wanda aka fara kera shi a shekarar 2016, an kammala shi ne a watan Maris.

Jirgin yakin mai tsawon mita 21 yana da tsananin gudu sosai saboda injina biyu da yake da shi.

KAAN yana da sauran wasu fasahohi kamar ba da bayanai kan yanayin da ake ciki da magance duk wata matsala da za ta jawo lalacewar wani abu, da tsara yadda yawan aikin matukin jirgin zai kasance.

TRT World