Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na Kyrgyztan Sadyr Japarov a Astana, babban birnin ƙasar Kazakhstan.
"Shugaba Erdogan, wanda ya je Astana don halartar Taron Ƙungiyar Ƙasashe masu magana da Turkanci (OTS), karo na 10, ya gana da Shugaba Sadyr Japarov na Kyrgyzstan," kamar yadda fadar shugaban ƙasar Turkiyya ya faɗa a shafin X a ranar Alhamis.
Ba a bayar da wani ƙarin bayani ba a kan yadda taron ya wakana.
Shugaban Turkiyyan ya isa Astana da wuri a ranar Alhamis din, don halartar taron OTS a ranar Juma'a da kuma yin wasu jerin ganawa da wasu ƙasashen.
An samar da Ƙungiyar OTS wacce a baya ake kiranta da Turkic Council ne a shekarar 2009, a matsayin wacce za ta haɗa kan ƙasashen da ke magana da yaren Turkanci don yin aiki tare da ƙarfafa dangantaka a tsakaninsu.
Mambobin ƙungiyar sun haɗa da Turkiyya da Azerbaijan da Kazakhstan da Kyrgyzstan da Uzbekistan, yayin da ƙasar Hungary da Turkmenistan da Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya suke da matsayin masu sa ido.
Muhimman batutuwan yankin
A watan da ya gabata ne, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya halarci wani taron Ministocin Wajen ƙungiyar OTS a Gidan Turkiyya da ke birnin New York na Amurka.
A yayin taron, sun tattauna batutuwan yankin da suka haɗa da yanayin da ake ciki a Karabakh.
Jami'an diflomasiyyar sun kuma tattauna batun "ayyukan yaƙi da ta'addanci na Azerbaijan" da kuma sake nazartar shirye-shiryen taro na gaba na OTS, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen ta fada a wata sanarwa.
An kuma tattauna alaƙar ƙungiyar da sauran manyan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa irin su Babban Zauren MDD da Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai OIC da kuma yadda za a ƙarfafa tsare-tsaren a wajen taron.